Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Gwamnatin jihar Kano na shirin samar da dokar da za ta bada cikakkiyar damar aiwatar da tsarin gudanar da aikin gwamnati ta amfani da fasahar sadarwa a duk fadin jihar, domin saukaka ayyukan gwamnati da bunkasa fannin tattalin arzikin ta amfani da fasahar sadarwa.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana haka ne a wajen rufe taron Majalisar Sadarwa, kirkira da fasahar sadarwa karo na 11, wanda ya gudana a dakin taro na Coronation dake gidan gwamnati Kano jiya Alhamis.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature ya aikowa Manhaja ya ce tsare-tsaren an samar da su ne da nufin tabbatar da daidaito, inganci, da kuma tabbatar da gaskiya wajen tafiyar da harkokin kudaden gwamnati ta hanyar amfani da manhajoji don tabbatar da taka tsantsan wajen amfani da kudaden.
Ya kara da cewa tun bayan hawansa mulki, gwamnan kano ya samu damar sake bude Cibiyar fasahar sadarwa da aka rufe, biyan albashi na hanyar zamani, inganta tsarin biyan kudin IGR da nufin toshe zurarewar kudade da dai sauransu.
Sannan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bukaci da a mikawa jihar Kano matattarar fasahar sadarwa ta NCC dake jihar domin yin amfani da shi yadda ya kamata, ya kuma kara jaddada kudirin gwamnatinsa na ci gaba da gudanar da ayyukan da za su ciyar da jihar Kano gaba musamman ta fuskar zamantakewa da tattalin arziki.
Tun da farko, ministan sadarwa, kirkire-kirkire da tattalin arziki ta fasahar sadarwa, Dakta Bosun Tijjani, ya ce an shirya taron ne bisa la’akari da ajandar sabunta fata ta Shugaba Tinubu, sanin karfin fasaha da kirkire-kirkire a matsayin masu samar da ci gaban tattalin arziki da kuma bunkasar tattalin arzikin Nijeriya.
Ya ci gaba da cewa, domin a kara habaka sauye-sauyen tattalin arzikin Nijeriya ta hanyar inganta samar da kayayyaki a sassa masu muhimmanci ta hanyar fasaha da kere-kere, an samar da wani tsari wanda ya kunshi ginshikai biyar na ilimi, manufofi, ababen more rayuwa, kirkire-kirkire, kasuwanci da jari.
Daga nan ne Dakta Bosun Tijjani ya ce kowane ginshiki na da nasaba da manufofin gwamnati da kuma cudanya da sauran jama’a, wanda shi ne tushen dabarun ba da damar ci gaban tattalin arziki da ci gaban fasahar sadarwa a kasar nan.
