Hukumar Ɗa’ar Ma’aikata ta fara tantance kadarorin manyan jami’an gwamnati

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar Da’ar Ma’aikata (CCB) ta fara tantance kadarorin masu rike da mukaman siyasa da kuma wasu manyan kadarorin gwamnati a wani bangare na yaki da cin hanci da rashawa da aka sabunta a kasar.

Shugaban riko na hukumar, Murtala Aliyu-Kankia, ya bayyana haka a lokacin da yake duba aikin tantancewar da ake yi a ranar Litinin a Katsina.

Ya ce atisayen zai shafi manyan jami’an gwamnati da ma’aikatan gwamnati da suka hada da sakatarorin dindindin, daraktoci da sauran manyan jami’an gwamnati.

By Editor