Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje, ya bukaci manyan abokan hamayyarsa a siyasa irin su Sanata Rabiu Kwankwaso da Gwamnan Kano Abba Yusuf da Sanata Ibrahim Shekarau da sauransu, su sauya sheka zuwa jam’iyyarsa.
Ganduje ya bukaci hakan ne bayan kammala taron masu ruwa da tsaki ranar Alhamis a Kano.
Ya ce dalilinsa na neman abokan hamayyar nasu su komo jam’iyyarsa, shi ne don a hadu a ciyar da kasa gaba karkashin jam’iyya guda wanda kuma hakan zai amfani al’ummar Jihar Kano.
Ya ba su tabbacin komai zai tafi daidai yadda ya kamata muddin suka sauya sheka zuwa jam’iyya mai mulki ta APC, musamman a jiharsu ta Kano.
A cewarsa, “Za mu iya amfani da wannan dama wajen samun ikon juya kasar a siyasance ta hanyar samun alkibla guda karkarshin jam’iyya daya.
“APC ita ce jam’iyya mafi girma a Afirka kuma ta yanke shawarar barin kofarta a bude don karbar sabbin mambobi,” in ji Ganduje.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin; tsohon Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai, Ado Doguwa; shugabannin APC na kananan hukumomi 44 APC da sauransu, na daga cikin wadanda suka halarci taron.
