Burina na sauke nauyin al’ummar da nake shugabanta – Hon. Baba-Goni

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Ƙaramar Hukumar Fune a Jihar Yobe, Hon. Baba-Goni Mustapha Bade ya ce babban burinsa shi ne ya sauke nauyin al’ummar da yake shugabanta, bayan da ya bayyana irin romon dimukradiyyar da ya samar tun bayan hawansa kujerar mulki a qaramar hukumar, inda ya bayyana cewa dukkan nasarorin sun samu ne bisa kyakkyawan jagorancin na Gwamna Mai Mala Buni.

Hon. Baba-Goni ya ce babban burinsa shi ne ya ga ya sauke nauyin da al’ummarsa suka dora mishi, ta hanyar ayyukan raya karamar hukumar da inganta rayuwar matasa, tsofaffi, yara da manya.

Ya ce shi ya sa suka vullo da shiryen kyautata jin dadin al’umma kamar tallafa wa masu karamin karfi da gidajen marayu, samar da ayyukan yi ga matasa a fadin kananan hukumomi.

“Samar da ingantattun cibiyoyin kiwon lafiya a cikin birane da karkara tare da majalisar yankin Fune da sauran kansilolin yanki 17 na jihar a karkashin fatan sabuntawa.

“Samar da ingantaccen ilimi a matakin firamare da sakandare don yara su samu ilimi mai inganci. Da kuma samar da ingantaccen ruwa da na’ura mai kwakwalwa da kuma gyara rijiyoyin burtsatse a dukkan gundomomi da kauyukan karamar hukumar Fune,” inji shi.

Vangaren tsaro kuma, Hon. Baba Goni ya bayyana kokarin da karamar hukumar ke yi wajen taimaka wa jami’an tsaro da ba su hadin kai ta fuskar ganawa akai-akai da shugabannin hukumomin tsaro a a karamar hukumar da suka hada da ‘yan sanda, ‘yan banga da soji da masu ruwa da tsaki; Hakimai, dagatai, shugabannin addinai da shugabannin al’umma.

Alhaji Baba-Goni Mustapha ya yaba wa gwamnatin Shugaba Buhari kan kafa hukumar Raya Arewa maso Gabas, inda ya bayyana cewa ci gaban da aka samu a yankin bai misaltuwa.

Ya ce matasa da dama sun samu ayyukan yi. Inda a karshe ya yi kira ga mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettim akan cewa a kodayaushe suna maraba da kowane irin aikin raya kasa da za a kai yankinsu.

Da karshe ya bai wa matasa shawara akan su rika mutunta dattijai a cikin al’ummarsu kasancewar su ne shugabanni na gaba.