Gomman mutane sun mutu a musayar wuta tsakanin sojoji da ‘yan bindiga a Filato

Spread the love

Bayanai daga Jihar Filato sun ce gomman mutane ne suka rasa rayukansu sakamakon dauki-ba-dadin da aka yi tsakanin sojoji da ‘yan bindiga a wasu kauyuka biyu da ke yankin Karamar Hukumar Mangu a jihar da safiyar ranar Asabar.

MANHAJA ta tattaro cewa an yi artabun ne bayan da Gwamnan Jihar, Caleb Mutfwang, ya sassauta dokar hana zirga-zirga na sa’o’i 24 da ya kafa a yankin tun farko.

Mutfwang ya ce sakamakon cigaban da aka samu game da sha’anin tsaro a yankin, ya sa ya sassauta dokar daga karfe  8 na safe zuwa 4 na rana.

Majiyarmu ta rawaito cewa, kimanin ‘yan bindiga 30 ne aka kashe yayin da wasu daga bangaren sojoji sun ji rauni a musayar wutar da aka yi a kauyukan Satguru da Tyop.

Wasu ganau da suka bukaci a sakaya sunansu, sun shaida wa majiyar tamu cewa, “Al’amarin ya afku ne tsakanin karfe 7 zuwa 7:30 na safe a lokacin da ‘yan bindigar suka zo da yawansu suka fara kai wa mutane hari a hanyar Gindri. Cikin kankanin lokaci aka sanar da sojoji abin da ke faruwa inda su kuma suka dira wurin ba da bata lokaci ba.

“Kimanin ‘yan bindiga 30 aka kashe, sannan an cafke wasu sama da 50 dauke da bindigogi da alburusai. Haka nan, wasu sojoji hudu sun tagayyara.”

Ya zuwa hada wannan rahoto, kakakin Rundunar  Operation Safe Haven mai aiki a yankin, ba ta kai ga cewa komai ba kan batun.

A lokutan baya-bayan nan, yankin Karamar Hukumar Mangu na daga cikin wuraren da ke fama da hare-haren ta’addanci a Jihar Filato, wanda gwamnatin jihar ke cewa tana kokarin ganin ta magance matsalar.

By Editor