Da Ɗumi-ɗumi: An rantsar da Ododo a matsayin sabon Gwamnan Kogi

An rantsar da Alhaji Ahmed Usman Ododo a matsayin zababben Gwamnan Jihar Kogi na biyar inda zai ja ragamar mulkin jihar na shekaru hudu masu zuwa.

Alkalin Alkalan Jihar, Mai Shari’a Josiah Mejabi ne ya jagoranci rantsar da Ododo a dandalin Muhammadu Buhari Civic Centre da ke Lokoja, babban birnin jihar a ranar Asabar.

Taron rantsarwar ya samu halartar dimbin masoya da magoya bayan sabon gwamnan, inda aka fara rantsar da Mataimakin Gwamna, Elder Joel Salifu Oyibo, kafin daga bisani Ododo ya sha tasa rantsuwar.

Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, shi ne ya wakilci Shugaban Kasa Ahmed Bola Tinubu a wajen bikin rantsarwar.

Ododo ya gaji wannan kujera ne daga Gwamna mai barin gado, Yahaya Bello, wanda ya yi mulkin jihar na tsawon wa’adi biyu.