Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Babban Bankin Nijeriya (wato CBN) ya buƙaci gwamnatocin jihohi su ƙara nuna tsauraran matakan kula da kashe kuɗi da karɓar bashi yayin da bankin ke shirin rungumar sabon tsarin da zai mayar da hankali wajen rage hauhawar farashi a ƙasar.
Mataimakin Gwamnan CBN mai kula da manufofin tattalin arziki, Muhammad Sani Abdullahi, ne ya bayyana hakan yayin wani taro da aka gudanar tare da jami’an gwamnatocin jihohi ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF).
Ya bayyana cewa sabon tsarin kula da hauhawar farashi ba zai yi nasara ba idan gwamnatocin jihohi suka ci gaba da kashe kuɗi ba tare da tsari ba.
“A cikin tsarin da ake mayar da hankali kan daidaita hauhawar farashi, duk wata kashe kuɗi mara tsari ko yawan bashi daga gwamnatocin jihohi na iya lalata ƙoƙarin da ake yi na tabbatar da daidaiton farashi,” inji Abdullahi.
Wannan gargaɗi na zuwa ne bayan da alƙaluman hauhawar farashi a Nijeriya suka sake tashi zuwa kaso 15.38 cikin ɗari a watan Maris na shekarar 2026, daga kaso 15.06 cikin ɗari da aka samu a watan Fabrairu, lamarin da ya kawo ƙarshen watanni 11 na raguwar hauhawar farashin kayayyaki.
Rahoton ya nuna cewa hauhawar farashin abinci ya ƙaru zuwa kaso 14.31 cikin ɗari daga kaso 12.12, yayin da farashin sufuri ya tashi zuwa kaso 16.9 daga kaso 14.7.
Babban Bankin ya kuma nuna damuwa cewa kashe kuɗaɗen yaƙin neman zaɓen shekarar 2027 da ake sa ran za su ƙaru na iya haddasa sabon tashin gwauron zabi na farashi idan ba a ɗauki matakan kariya ba.
Muhammad Sani Abdullahi ya bayyana muhimman abubuwa huɗu da ake sa ran jihohi za su mayar da hankali a kai ƙarƙashin sabon tsarin.
Ya ce ya zama dole jihohi su tabbatar da tsauraran matakan kula da kuɗi, su karɓi bashi cikin hikima bisa tsarin dogon lokaci, su inganta sarrafa kuɗaɗe da basussuka, sannan su ƙarfafa hanyoyin samun kuɗaɗen shiga na cikin gida.
Haka kuma, ya buƙaci jihohi su rage dogaro da bashin gaggawa, su inganta tsarin kasafin kuɗi tare da tabbatar da cewa duk wani sabon bashi ya yi daidai da ƙarfin da za a iya biya ba tare da haddasa matsalar tattalin arziki ba.
Daraktan Sashen Manufofin Kuɗi na CBN, Victor Oboh, ya bayyana sabon tsarin da ake son aiwatarwa a matsayin tsarin da zai amfani kowa, yana mai cewa zai taimaka wajen ƙarfafa amincewar jama’a ga manufofin gwamnati tare da daidaita tsammanin kasuwa.
Sai dai ya jaddada cewa Babban Banki kaɗai ba zai iya tabbatar da daidaiton farashi ba a ƙasar da ke da tsarin tarayya irin na Nijeriya.
Shi ma Daraktan Manufofi da Bincike na ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya, Olalekan Yunusa, ya yaba da fara tattaunawar tun da wuri, yana mai cewa sauya tsarin daga kula da yawan kuɗi zuwa mayar da hankali kan rage hauhawar farashi na nuna aniyar gwamnati na ɗora tattalin arzikin ƙasa a kan turba mai ɗorewa.
Taron ya samu halartar jami’ai daga fiye da jihohi 20, ciki har da kwamishinonin kuɗi, manyan akantoci da shugabannin hukumomin ƙididdiga.
Mafi yawan mahalarta taron sun nuna goyon bayansu ga sabon tsarin sauye-sauyen da CBN ke son aiwatarwa tare da alƙawarin ba da haɗin kai domin ganin an samu nasara.
