NDLEA ta kama hodar iblis ta biliyoyin naira a hannun wasu nakasassu

Spread the love

Hukumar Hana Sha Da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA), ta kama wasu mutane uku masu larura bisa zargin safarar miyagun ƙwayoyi a wasu samame daban-daban da aka gudanar a jihohin Anambra da Kwara.

A cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na hukumar, Femi Babafemi, ya fitar ranar Lahadi, ya bayyana cewa jami’an hukumar sun bi sahun wani mutum mai shekaru 60 mai suna Romanus Nwabara har zuwa dajin Akpaka da ke Onitsha a Jihar Anambra, inda suka kama shi da giram 250 na tabar wiwi nau’in skunk da aka shirya cikin ƙananan ledoji domin sayarwa.

A wani samame daban da aka kai Ogbunike, shi ma a Jihar Anambra, jami’ai sun kama wani mutum mai shekaru 25 mai suna Amos Kenneth, wanda shi ma mai larura ne, tare da giram 160.3 na Tramadol, ƙwayoyin Diazepam guda 80, giram 38.23 na Eɗol-5 da gram 176.93 na skunk.

A Jihar Kwara kuma, jami’an NDLEA da ke sintiri a kan titin Bode Saadu sun tare wata motar haya inda suka gano kilo 6.3 na skunk da aka ɓoye a cikin jakar makaranta mai launin ruwan ƙasa mallakin wani fasinja mai suna Usman Salisu, wanda shi ma nakasashe ne.

Babban nasarar da hukumar ta samu kuwa ita ce a Lekki Phase 1 da ke Legas, inda jami’an sashen ayyuka na musamman na NDLEA suka kai samame wani katafaren gida da ake zargin ana amfani da shi wajen ɓoye miyagun ƙwayoyi.

A yayin samamen, jami’an sun kwato buhuna 4,000 na wata irin tabar wiwi mai ƙarfi da ake kira “Loud”, wadda aka shigo da ita daga ƙetare. Nauyin ƙwayar ya kai kilo 2,326, kuma an kiyasta kuɗinta a kasuwa ya haura naira biliyan 5.815.

Haka kuma an ƙwace motocin bas guda biyu na Mercedes-Benz tare da wasu kayayyakin haɗa fakiti na alfarma da ake zargin ana amfani da su wajen rarraba ƙwayoyin a kasuwa.

A wani wuri daban kuma, jami’an NDLEA sun kama Emmanuel Osita Okeke mai shekaru 38 a Nyanya-Karu da ke Jihar Nasarawa tare da kilo 129 na skunk.

Hakazalika, a wani samame da aka gudanar a kan titin Okene-Lokoja da ke Jihar Kogi, jami’ai sun tare wata motar haya da ke kan hanyarta ta zuwa Abuja inda suka gano manyan buhuna 76 na skunk masu nauyin kilo 766.

An kama mutane uku da suka haɗa da Mathew Omohove, Ebuka Desmond da Babangida Musa dangane da lamarin.

A yankin Ijora Badia kuma, jami’an NDLEA sun kai samame wata cibiyar sarrafa wani sinadari mai maye da ake kira skuchies, inda suka kama wasu mutane biyu masu suna Bose Jamiu da Gbenga Gege.

Ana zargin mutanen da sarrafa tabar wiwi tare da haɗa ta da wasu sinadarai masu illa. Jami’an sun kwato lita 270 na sinadarin da aka haɗa, wanda aka fi sani da skuchies, tare da gram 106 na Tramadol.

Baya ga samamen kama masu safarar miyagun ƙwayoyi, hukumar ta ce tana ci gaba da yaƙin wayar da kai kan illar shaye-shaye ta hanyar shirinta mai suna “War Against Drug Abuse (WADA)” a makarantu, al’ummomi, wuraren aiki da kuma cibiyoyin gargajiya a faɗin ƙasar nan.

An gudanar da shirye-shiryen wayar da kai a jihohin Nasarawa, Ekiti, Enugu, Abia, Legas, Akwa Ibom, Kano da Oyo.

Shugaban NDLEA kuma Babban Daraktan Hukumar, Mohamed Buba Marwa, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da ayyukan bisa jajircewarsu wajen rage yawaitar miyagun ƙwayoyi tare da ci gaba da wayar da kan jama’a kan illar shaye-shaye.

Ya kuma buƙaci jami’an hukumar a faɗin ƙasar nan da su ci gaba da ƙara ƙaimi a yaƙin da ake yi da safarar miyagun ƙwayoyi.

By ukarofi