Farashin mai ya tashi bayan Trump ya yi watsi da sharuɗɗan Iran

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMAMD

Farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya ya yi tashin gwauron zabi bayan Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya yi watsi da sabbin sharuɗɗan da Iran ta gabatar domin kawo ƙarshen rikicin Gabas ta Tsakiya.

Trump ya bayyana martanin Iran ga tayin zaman lafiya da Amurka ta gabatar a matsayin “abin da ba za a amince da shi ba ko kaɗan,” lamarin da ya ƙara tayar da hankulan duniya kan yiwuwar sake ɓarkewar rikici bayan makonni ana tattaunawar diflomasiyya.

A wani saƙo da ya wallafa a dandalinsa na sada zumunta na Truth Social ranar Lahadi, shugaban na Amurka ya ce, “Na karanta martanin da wakilan Iran suka bayar. Ban yarda da shi ba — gaba ɗaya ba abin karɓa ba ne.”

Ko da yake Trump bai bayyana cikakken bayanin tayin Iran ba, rahotanni sun nuna cewa Tehran ta nemi tabbacin kariya kan tarin sinadarin uranium da ta tace tare da buƙatar dakatar da rikice-rikice a yankin, musamman a ƙasar Lebanon.

Shi ma Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya nuna cewa ƙasarsa ba za ta miƙa wuya ba duk da ci gaba da tattaunawa.

“Ba za mu taɓa rusuna wa abokan gaba ba. Tattaunawa ko sulhu ba yana nufin miƙa wuya ko ja da baya ba ne,” kamar yadda ya wallafa a shafinsa na ɗ.

Rahotanni daga gidan talabijin na gwamnatin Iran, IRIB, sun ce an miƙa martanin Tehran ga Amurka ta hannun masu shiga tsakani daga Pakistan, inda aka fi mayar da hankali kan dakatar da rikicin a dukkan fannoni, ciki har da yaƙin da ke da nasaba da ƙungiyar Hezbollah a Lebanon, tare da neman tabbacin tsaron hanyoyin ruwa.

A nasa ɓangaren, Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ce ba za a kawo ƙarshen yaƙin ba har sai an rusa cibiyoyin nukiliyar Iran tare da fitar da sinadarin uranium ɗinta daga ƙasar.

“Har yanzu ba a gama ba, domin akwai sauran sinadarin uranium da aka tace wanda dole ne a fitar da shi daga Iran,” inji Netanyahu a wata hira da shirin “60 Minutes” na CBS.

Jaridar The Wall Street Journal ta ruwaito cewa Iran ta ba da shawarar rage ƙarfin wani ɓangare na uranium ɗinta tare da tura sauran zuwa wata ƙasa ta uku, matuƙar za a ba ta tabbacin dawo da su idan tattaunawar ta rushe ko Amurka ta fice daga yarjejeniya.

Rahotanni sun tuna cewa rikicin ya fara ne tun ranar 28 ga Fabrairu lokacin da Amurka tare da haɗin gwiwar Isra’ila suka kai hari Iran, wanda ya yi sanadin mutuwar Jagoran Addini na ƙasar da wasu manyan jami’an gwamnati.

Tun bayan cigaba da rashin cimma matsaya tsakanin ɓangarorin biyu, farashin mai ya ƙaru da sama da dala huɗu kan kowace ganga a ranar Litinin, musamman saboda ci gaba da tangarɗar zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz, wata muhimmiyar hanyar da ke ɗaukar kusan kashi ɗaya cikin biyar na man duniya da iskar gas kafin rikicin ya ɓarke.

Wata babbar mai nazarin kasuwa a kamfanin Phillip Noɓa, Priyanka Sachdeɓa, ta shaida wa Reuters cewa kasuwar mai na ci gaba da sauyawa ne bisa kalaman shugabanni da matakan siyasa daga Washington da Tehran.

Ta ce, “Kasuwar mai yanzu tana tafiya ne bisa tasirin kalaman siyasa, inda farashi ke tashi ko sauka da zarar an samu wata sanarwa ko gargaɗi daga Amurka ko Iran.”

By ukarofi