Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Alƙaluman hauhawar farashin kayayyaki na baya-bayan nan sun tayar da hankali a tsakanin masana tattalin arziki da masu tsara manufofin tattalin arziki, inda fitaccen masanin harkokin kuɗi, Bismarck Rewane, Manajan Darakta na Kamfanin Samar da Kuɗaɗe (FDC), ya yi gargaɗin cewa ci gaba da hauhawar farashin kayayyaki na nuni da matsalolin rashin tsari da ɓangaren tattalin arzikin Nijeriya ke fuskanta.
Da yake magana a shirin Morning Business a gidan Talabijin na Channels a ranar Litinin, Rewane ya yi nuni ga sabbin alƙaluman hauhawar farashin kayayyaki, wanda ya nuna tashin hankali a cikin hauhawar farashin kayayyaki na wata-wata.
“Idan ka dubi lambobi na ƙarshe na hauhawar farashin kayayyaki, ainihin hauhawar farashin kayayyaki ya ƙaru, kuma hauhawar farashin wata-wata ya ƙaru sosai. Wannan yana nufin cewa akwai batutuwan rashin tsarin da ya kamata a kula da su,” inji shi.
Rahoton da hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ta fitar ya nuna cewa hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu zuwa kashi 23.18 a watan Fabrairun 2025, inda ya ragu daga kashi 24.1 cikin 100 a watan Janairun 2025.
Rewane ya jaddada cewa a lokacin da hauhawar farashin kayayyaki ya ƙaru a cikin tattalin arziki, komai sauyawa ya ke yi. Hauhawar farashin kayan gini ya samo asali ne daga taɓarɓarewar hanyoyin samar da wutar lantarki, aarancin wutar lantarki, rashin ababen more rayuwa, da rashin daidaiton kasafin kuɗi — abubuwan da Nijeriya ta yi fama da su tsawon shekaru.
“Da zarar an samu hauhawar farashin kayayyaki a cikin ƙasa, ba zai ɗauki lokaci mai tsawo ba kafin komai ya tashi,” inji shi.
