Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Kula da Hada-hadar Hannayen Jari ta ƙasa (SEC) ta ƙara jaddada ƙudirinta na kare masu zuba jari a kasuwannin hannayen jari na Nijeriya, ta hanyar zafafa ƙoƙarin kawar da ayyukan ’yan damfara.
Hukumar ta sha alwashin sanya hukunci mai tsauri a kan ma’aikatan da ba su da gaskiya a wani ɓangare na murƙushe ayyukan damfara.
Da yake magana a kan shirin, Darakta Janar na SEC, Dokta Emomotimi Agama, ya jaddada matsayin hukumar na rashin yarda da zamba a kasuwa, yana mai gargaɗkn cewa marasa gaskiya za su fuskanci mummunan sakamako.
“Don haka, a fili a gare mu, yana sa mutane su fahimci cewa babu wata mafaka ga duk wanda ke da niyyar damfarar ‘yan Nijeriya masu saka hannun jari a wannan kasuwa,” inji Dokta Agama.
Ya jaddada cewa dokar zuba jari da tsaro (ISA) 2007 tana aiki ne a matsayin tsarin doka da ke jagorantar tsarin tsaro a Nijeriya, tare da tabbatar da cewa masu gudanar da kasuwa sun cika ƙa’idojin ɗa’a.
