Matasa sun daka wawa kan abincin da Seyi Tinubu ke rabawa a Gombe

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wasu fusatattun matasa sun wawushe abincin da aka yi niyyar raba wa na watan Ramadan a jihar Gombe, wanda rahotanni suka ce ya fito daga wajen ɗan shugaban Nijeriya, Seyi Tinubu.

Seyi dai yana rangaɗi a wasu jihohi da ke arewacin ƙasar, inda yake haɗuwa da mazauna jihohin da kuma shugabannin siyasa wajen buɗa-baki.

Wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta, ya nuna matasan na wawason katan-katan na kayan abinci daga kan wata mota da ke tsaye a bakin titi.

An hangi matasan na harba wa waɗanda ke ƙasa kayan abincin, inda suke karɓa suke kuma yin gaba.

Kayan abincin sun haɗa da buhunan shinkafa da sikari da mai da kuma gishiri.

Yayin da aka raba ɗaya daga cikin motocin ɗauke da kayan abincin, matasan sun tare guda inda suka yi wawason komai da ke cikinta.

By ukarofi