An yi jana’izar wasu ma’aurata Dozie da Joan Okoye, waɗanda suka rasa rayukansu a wani mummunan hatsarin mota da wata tankar iskar gas ta janyo a ranar 11 ga Maris, 2025.
Ma’auratan sun yi aure ne makonni kaɗan da suka gabata, a ranar 22 ga watan Fabrairu.
Sun rasu ne a wani mummunan harin da ya afku a kan gadar Otedola da ke kan hanyar Legas zuwa Ibadan.
Wani faifan bidiyo da aka yi ta yaɗawa a shafukan sada zumunta ya nuna masu makoki sun cika da alhini yayin da suke bankwana da matasan ma’auratan.
Da dama dai sun karkata zuwa shafukan sada zumunta domin jajantawa tare da yin kira da a ɗauki tsauraran matakan tsaro don hana afkuwar irin wannan bala’i.
Yayin da ‘yan uwansu ke makoki, tunawa da Dozie da Joan Okoye ya bazu ko ina.
Da take yaɗa bidiyon a shafinta na Instagram, ‘yar jarida mai bincike Temilola Sobola ta rubuta; “Wannan ita ce Chiedozie, ma’aikaciyar bankin Zenith da Chidalu, ma’aikacin jinya daga Amurka, sun yi aure a Legas a ranar 22 ga Fabrairu, 2025. Abin takaici, sun mutu sakamakon fashewar tankar iskar gas da ta afku a gadar Otedola a ranar 11 ga Maris, 2025. An yi jana’izar su duka a 22 ga Maris, 2025. Iyali da abokan arziki na cikin alhini.”
