NDLEA ta kama ’yar Indiya da hodar iblis cikin ledar cakulan a Kano

Spread the love

Jami’an Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA), sun damƙe wata mata ‘yar ƙasar Indiya mai suna Neetu Neetu ‘yar shekaru 42 a filin jirgin saman Malam Aminu Kano ɗauke da fakiti 72 hodar iblis da aka rufe a matsayin cakulan.

An gano wani nau’in hodar mai nauyin kilogiram 11 a cikin jakunkuna Neetu bayan binciken kwakwaf, biyo bayan sahihin bayanan sirri, a lokacin da jirgin ƙatar Airways ya yi jigilar QR1431 daga Bangkok, Thailand zuwa ɓietnam da Doha a filin saukar jiragen sama na Kano ranar Juma’a 14 ga Maris 2025.

Kame Neetu na nuni da yunƙurin da ƙungiyoyin masu fataucin miyagun ƙwayoyi ke yi na ɗaukar hayar mata farar fata da ‘yan ƙasashen waje wajen ɗaukar haramtattun kwayoyi ta kan iyakokin Nijeriya, yunƙurin da jami’an NDLEA suka yi ta ci gaba da kamawa da taimakon kayayyakin fasahar zamani da kuma bayanan sirri, inji Shugaban Hukumar NDLEA, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (Mai Titaya).

A wani samame da jami’an NDLEA suka yi a Kano, a ranar Alhamis 20 ga watan Maris, sun kama wani mutum mai shekaru 45 da ake zargi, Michael Ogundele, ɗauke da silindar iskar gas mai nauyin lita 50 a Gadar Tamburawa, kan hanyar Zaria zuwa Kano.

Dangane da ingantaccen bincike, daga baya aka yi amfani da kayan aikin walda don yanke ƙatuwar silindar bayan haka an fitar da kwayoyi 50,000 na tramadol 225mg da aka ɓoye a ciki.

Yayin da aka kama Sunday Ogar, mai shekaru 40 a unguwar Gunduwawa da ke Kano a ranar Laraba 19 ga watan Maris ɗauke da skunk mai nauyin kilogiram 27, wani nau’in tabar wiwi, wata mace mai suna Khadijah Abdullahi, mai shekaru 40, an kama ta da kwalaben maganin codeine 424 a unguwar Lungun Bulala Yalwa da ke jihar a ranar Talata 18 ga watan Maris.

A Legas, an kama su biyu Olumuyiwa Kolawole da Samod Adisa da skunk 67.5kg a Mushin a daidai lokacin da aka kwato 100.8kg na sinadari guda 100.8 a ma’ajiyar wasu mutane biyu da suka gudu a unguwar Anifowoshe da ke Mushin yayin da aka kama Isah Idris a Apapa da skunk 4.5kg; 600gram na tramadol 225mg da lita 30 na maganin codeine a ranar Talata 18 ga Maris. Wani wanda ake zargi mai suna Yahaya Mohamed, an kama shi ne a ranar a unguwar Ikotun da ke jihar dauke da nau’o’in hodar iblis da tabar heroin da kuma methamphetamine.

By ukarofi