Mai ya sa ka ke ƙarya a Ramadan – Wike ga Atiku kan zaɓen 2023

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Ana cigaba da faɗi-in-faɗa a tsakanin tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da Ministan Abuja Nyesom Wike game da zaɓar mataimakin na farkon a zaɓen 2023.

Manyan ƴaƴan Jam’iyyar PDP’n sun samu rabuwa ne a lokacin da kowane ɗaya daga cikin su ya nemi zama ɗan takarar jam’iyyar a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023, inda Atiku ya zo na ɗaya tare da zaɓar tsohon gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa a matsayin mataimaki a gare shi madadin Wike da ya zo na biyu a zaɓen fidda gwani.

A baya, Atiku ya ce ya zaɓi tsohon gwamnan na Delta ne ba kaɗai don son yin aiki da shi ba, har ma da kasancewar sa mai nagartar da zai iya zama shugaban ƙasa.

A yayin wata hira da aka yi da shi a kwanan nan ne kuma, Atiku ya faɗi wasu kalamai akasin waɗancan, inda ya ce ya ɗauki Okowa ne a matsayin abokin tafiyarsa sakamakon zaɓar masa shi da kwamitin jam’iyyar ya yi.

Saidai, Wike ya musanta wannan batu da cewa, ƙarya ne tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya yi a watan Ramadana.

A wata takarda da jami’in hulɗa da jama’arsa, Lere Olayinka ya fitar, Wike ya ce, abin takaici ne a ce Atiku ba zai ƙaurace wa yin ƙarya a wata mai alfarma ba, ya na mai cewa ya yi mamaki a ce kwamiti ya gabatar masa da ɗan takara mai ƙuri’a biyu a madadin mai 13.

Jami’in ya ce, Wike bai nemi zama mataimaki ga Atiku ba, saidai shi Atikun ne ya nemi hakan, kuma Wiken ya amince tare da gabatar masa da wasu sharuɗɗa.

Lallai kwamitin Wike ya zaɓa a matsayin wanda zai samu muƙamin, inda daga bisani ya zaɓi Okowa bisa wasu dalilai da ya dogara da su, kamar yadda Olayinka ya bayyana.

Ya kuma kafa masa hujja da hadisin Manzon Allah (SAW) da ke cewa duk wanda bai kame kansa daga kalaman ƙarya ba a watan Ramadana, to Allah ba ya buƙatar ya ajiye abinci ko abin shansa, ya na mai cewa duk da haka sai da Atiku ya yi ƙarya.

Kazalika, ya shawarci Atiku da ya zama mai faɗar gaskiya a zantukansa, saboda a yanzu Wike bai damu da abin da ya wuce na 2023 ko son zama mataimakin shugaban ƙasa.

By Babaji