Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ta bayyana cewa hauhawar farashin kaya a Nijeriya ya ƙaru zuwa kashi 34.60 cikin 100 a watan Nuwamban 2024, wanda ya nuna ƙaruwar kashi 0.72 cikin ɗari idan aka kwatanta da na Oktoba na 33.88 bisa ɗari.
Hukumar NBS ta bayyana hakan ne a cikin rahotonta na farashin kayayyaki (CPI) da kuma hauhawar farashin kayayyaki na watan Nuwamba, wanda aka fitar a Abuja ranar Litinin.
A duk shekara, adadin hauhawar farashi a watan Nuwamba 2024 ya kasance kashi 6.40 bisa ɗari fiye da kashi 28.20 da aka samu a watan Nuwamba 2023.
Rahoton ya kuma bayyana cewa, a duk wata, hauhawar farashin kayayyaki a watan Nuwamban shekarar 2024 ya kai kashi 2.63, wanda ya ɗan yi ƙasa da kashi 2.64 cikin ɗari da aka samu a watan Oktoba.
Hukumar ta NBS ta danganta hauhawar farashin kayayyaki a sassa daban-daban da suka haɗa da abinci da abubuwan sha, gidaje, ruwa, wutar lantarki, iskar gas, tufafi, sufuri, ilimi, lafiya da sauran kayayyaki da ayyuka.
Matsakaicin CPI na watanni 12 da suka ƙare Nuwamba 2024 ya tsaya a kashi 32.77 cikin ɗari, wanda ke nuna ƙaruwar kashi 8.76 cikin ɗari daga kashi 24.01 cikin ɗari da aka samu a watan Nuwamba 2023.
Farashin abinci a watan Nuwamba 2024 ya tashi zuwa kashi 39.93 bisa ɗari a kowace shekara, daga kashi 32.84 cikin ɗari a cikin Nuwamba 2023.
An danganta hauhawar farashin kayan abinci da tsadar doya, shinkafa, masara, da sauran kayan abinci, da kuma man kayan lambu, mai, da abinci da aka sarrafa.
A duk wata-wata, hauhawar farashin abinci ya ƙaru da kashi 2.98, wanda ya dan kaɗan daga kashi 2.93 da aka samu a watan Oktoban 2024.
