
Daga Umar Aƙilu Majeri a Dutse
Kamar yadda binciken ƴan sanda ya tabbatar, sun gano cewa ciwon haukan gado ne ya sa wata mata mai kimanin shekaru 40 mai suna Fatsuma Bagobiri ta banka wa kanta wuta a ƙauyen Garin Mallam da ke Ƙaramar Hukumar Guri ta Jihar Jigawa.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan Jihar Jigawa, DSP Lawan Shiisu Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce, an samu rahoton faruwar lamarin ne a safiyar ranar Alhamis da ta gabata kuma jami’an ofishin ƴan sanda na shiyyar Guri sun gaggauta kai wa matar ɗauki a lokacin da suka samu bayanin ta je daji ta bankawa kanta wutar.
Ya kuma ma tabbatar da cewa, tuni jami’an ƴan sanda suka kai matar asibiti inda likitoci suka tabbatar da mutuwarta kuma daga bisani aka miƙa gawar ta ga iyayanta domin yi mata jana’iza.
Binciken farko da aka yi ya nuna cewa marigayiyar ta shiga cikin damuwa ne tun lokacin da ta rabu da aurenta a watannin baya.
Kwamishinan ƴan sandan jihar, CP AT Abdullahi, ya buƙaci jama’a su riƙa miƙa al’amuransu ga Allah Ta’ala gami da yin addu’ar neman albarka da kuma neman shawara a wajen manya akan al’amura masu sarƙaƙiya ba su ke riƙa zartar wa kansu hukuncin ba.
Ya ce, irin wannan mummunan yanayi da ake tsintar kai a ciki ya sanya ya ke da mahimmanci a riƙa duba lafiyar ƙwaƙwalwa da kuma neman taimakon makusanta.
