Gundogan ya sake dawo wa Manchester City

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Ƙungiyar Manchester City ta ƙasar Ingila ta sake ɗaukar ɗan wasa Ilkay Gundogan daga ƙungiyar Barcelona.

Ɗan wasan na ƙasar Jamus ya rattaɓa hannu a kwantiragin shekara ɗaya bayan ya bar ƙungiyar a shekarar 2023.

Gundogan mai shekaru 33 yayi nasarar lashe kufuna 12 cikin shekaru bakwai da yi a zangonsa na farko a matsayin ɗan wasan Man City ciki har da firimiyar Ingila guda biyar da kuma kofin zakarun Nahiyar Turai guda ɗaya a shekarar 2023.

Ɗan wasan ya ce ya ji daɗin kasancewar sa a Manchester City a halin fafatawa da kuma akasin haka ganin yadda ya samu sabo da magoya bayan ƙungiyar.

Ya ƙara da cewa, ya ji daɗin dawowarsa ƙungiyar kasancewar ya na girmama koci Pep Guardiola a matsayinsa na wanda ya fi kowane koci iya horarwa a fagen ƙwallon ƙafa.

Game da batun barin ƙungiyar Barcelona, ɗan wasan ya ce, ya je can ne da nufin tsawaita zamansa, amma sakamakon matsalolin kuɗi da ƙungiyar ke fuskanta ya sa yanke shawarar komawa City bayan shekara ɗaya a ƙungiyar.

By Babaji