Tinubu ya naɗa Sanata Barau shugaban kwamitin raba kayan tallafi na Kano

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Mataimakin shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Barau Jibrin a matsayin shugaban kwamitin shugaban ƙasa na raba kayan tallafin rage raɗaɗin talauci ga al’ummar jihar Kano.

Sanata Barau ya faɗi haka ne a wani zama inda ya ce kasancewar ana zargin sauya akalan wasu kayayyakin tallafi na al’ummar Kano ya sanya aka ƙirƙiri sabon kwamitin.

Ya ce, kwamitin na da wakilci daga jam’iyyun APC, PDP da NNPP da majalisar mashawarta na jam’iyyu (IPAC) da kuma sarakunan gargajiya.

An yi da zaman ne musamman kan yadda za a gudanar da raba tallafi ga mabuƙata na Kano inji Sanatan.

Ya ce, Shugaba Tinubu ya nuna damuwarsa kan yadda ba a yin rabon yadda ya dace.

Kazalika, ya ce za a yi jadawalin waɗanda za su ci gajiyar tallafin inda kowannensu zai samu shinkafa buhu guda mai nauyin 25kg bayan tantancewa na bada ɗaya daga cikin katin shaidar ƙasa kamar na ɗan ƙasa, na zaɓe ko na tuƙi.

By Babaji