NELFUND ya samu ƙarin biliyan N50 daga EFCC

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Ofishin asusun bada aron kuɗin karatu ga ɗalibai, NELFUND ya samu shaidar ƙarin kuɗi da adadinsa ya kai Naira biliyan 50 daga hukumar hana yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta’annati (EFCC).

‘News Agency Nigeria’ ya ruwaito cewa Gwamnatin Tarayya ta bai wa ofishin Naira biliyan 60.

Daraktar yaɗa labarai ta NELFUND, Oseyemi Oluwatuyi ta faɗi haka acikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma’a.

Ta ce kuɗin da EFCC ta bayar ya biyo bayan umarni ne da Shugaba Tinubu ya bai wa hukumar a ranar 4 ga watan Agusta don a bunƙasa shirin bada aron kuɗin ga karatun ɗaliban makarantun gaba da sekandire.

Ta ƙara da cewa hakan da Shugaba Tinubu yayi, wani mataki ne na ƙoƙarin gwamnatinsa wajen ganin an sauƙaƙe hanyoyin samun ilimin ga al’ummar Nijeriya, ta mai cewa za a cigaba da gudanar da shirin don ya isa dukkan ɓangarorin al’ummar ƙasa la’akari da yawansu.

By Babaji