
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Shugaba Bola Tinubu ya jaddada aniyarsa ta cigaba da inganta kiyaye dokar ƙasa da sauƙaƙe shugabanci na adalci a Nijeriya.
Tinubu ya faɗi haka ne a lokacin bikin rantsar da sabuwar Alƙalin Alƙalan Nijeriya (CJN) ta riƙon ƙwarya, Kudirat Kekere-Ekun a Fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Shugaba Tinubu ya bayyana yadda gwamnatinsa ke ƙoƙari wajen saduakarwa ga kiyaye dokar ƙasa tare da tabbatar da an bai wa ɓangaren alƙalanci goyon bayan da ya ke buƙata saboda matsayin muhimmancin sa a wajen al’ummar ƙasa da zaman lafiyar su.
Ya yi kira ga Kekere-Ekun ta tsare aikinta wajen tabbatar da gaskiya da adalci a lokacin gudanar da harkokin ofishinta.
Ya kuma jinjina mata kan ƙoƙarin da ta yi a baya na tsare aikinta da jajircewa gami da amfani basira wanda hakan ya kai ta ga matsayin da ta tsinci kanta a halin yanzu.
Tinubu ya ƙara da yaba wa ƙoƙarin kotun ƙoli na samar da sauye-sauye masu kyau a Nijeriya, warware rikicin Shari’a masu tsauri da daidaita tsarin gudanarwa, ya na mai fatan ta dore akan haka don amfanin Nijeriya da al’ummarta.
Ya kuma yi godiya ga Mai Shari’a Kayode Ariwoola na hidima da ya yi tsawon shekaru 33 ga harkokin Shari’a da ma ƙasa baki ɗaya, ya mai masa fatan alheri.
