HIKAYATA 2021: Agusta 22 za a rufe shiga gasar

Daga BASHIR ISAH

Ya zuwa ranar 22 ga Agusta ake sa ran rufe shiga gasar rubutun ƙagaggen labari ta mata mai taken ‘Hikayata’ ta 2021 wadda sashen Hausa na BBC ya saba shiryawa duk shekara.

Sanarwar da BBC ta fitar ta nuna an ƙirƙiro gasar ƙagaggen gajeren labarin ce a 2016 don ƙarfafa wa mata wajen bayarwa da kuma yaɗa labarun da suka shafe su.

Sanarwar ta ce akan bai wa mata damar aiko da ayyukansu na ƙagaggun labarai da suka rubutu cikin harshen Hausa masu yawan kalmomi tsakanin 1000 zuwa 1500.

Bayan kammala tattara ayyukan da aka shigar a gasar, akan miƙa su ga alƙalan gasa don su yi aikinsu inda a ƙarshe sukan zaɓi labari guda wanda ya zama zakara da kuma wanda ya zo na biyu da na uku.

Editan Sashen Hausa na BBC, Aliyu Tanko, ya ce, “Mun samu tarin nasarori dangane da wannan gasa tun bayan da aka assasata shekaru shida da suka gabata. Gasar Hikayata ta zame wa mata da dama murya da kuma damar baje kolin fasaharsu.

“A bara ayyuka 400 aka shigar a gasar daga sassan duniya, kuma ina sa ran na bana su zarce haka.”

A nasa ɓangaren, Shugaban Sashen Harsunan Afirka ta Yamma na BBC, Oluwatoyosi Ogunseye, bayyana farin cikinsa ya yi dangane da irin karɓuwar da gasar Hikayata ta samu, don haka ya ce za su ci gaba da mara wa gasar baya yadda ya kamata.

Maryam Umar, ‘yar shekara 20 daga Sakkwato, ita ce ta lashe gasar a bara inda labarinta mai taken “Rai da Cuta” ya zo na ɗaya. Labarin da ya ƙunshi bayani a kan Azima da maigidanta game da abin da ya shafi cutar korona.

Maryam ta ce, ‘’Gasar Hikayata ta zama tamkar mabuɗin nasara ga rayuwarta, na samu buɗi da dama wanda ban san da da su ba. Nasarar ta sanya ni zama tauraruwa kuma mai arziki da kuma iya dogaro da kai. Don haka ina kira ga ‘yan’uwa mata da su gyara alƙalaminsu.”

Sanarwar ta ce, ga masu buƙatar shiga gasar sai su hanzarta su aika da ayyukansu ta wannan adireshi :
[email protected] tun kafin a rufe hanya a ranar 22 ga Agustan da ake ciki.

A ƙarshe, za a miƙa kyaututtuka ga duk wadda ta zo ta ɗaya da kuma mutum biyu da ke biye da ita a wajen taron karramawa da za a gudanar a Nuwamba mai zuwa.