Ruftawar gada ta yi sanadin mutuwar matafiya 21 a Jigawa

Daga UMAR AƘILU MAJERI a Dutse

Sakamakon ruwan sama mai yawa da aka samu a wasu sassan jihar Jigawa hakan ya haifar da ruftawar gadar da ta haɗa Basirka da Gwaram da jihohin Bauchi, Adamawa da Borno.

Ruftawar gadar ta yi sanadin faɗawar wasu motoci guda biyu wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 21 tare da jikkata matashi guda.

Bayyanar jami’an tsaro a inda ibtila’in ya auku haɗa da ƙokarin jama’ar yankin, hakan ya taimaka matuƙa wajen fitar da gawarwakin matafiyan da haɗarin ya rutsa da su.

Ya zuwa haɗa wannan labari, ba kai ga kammala tantance waɗanda suka rasun ba baki ɗaya.

Da yake jawabi a lokacin da ya kai ziyarar gani da ido a inda lamarin ya faru, Mataimakin Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namaddi, ya ce gwamnatin jihar na duba yiwuwar gyara gadar da ta rushe duba da cewa hanya ce muhimmiya da ta haɗa jihohin Borno da Taraba da Adamawa da sauransu.

Namaddi ya tabbatar da mutuwar mutun 21 a haɗarin, tare da cewa mutum guda na kwance a asibitin Basirika ana ci gaba da yi masa magani sakamakon raunin da ya ji. Ya ce gwamnati na ci gaba da tuntuɓar ‘yan’uwan waɗanda suka rasu domin a yi musu jana’iza.

A wata sabuwa, ambaliya ta mamaye ƙauyen Dingaya a jihar sakamakon ruwan saman, lamarin da ya kai ga jama’ar ƙauyen sun fice daga gidajensu don neman mafaka a wasu wurare.

An ce gidaje sama da140 ne suka lalace a ƙauyen sakamakon ambaliyar, wanda ya haifar da magidanta da iyalansu sun koma kwana a tashar mota, makarantun gwamnati da sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *