Da Ɗumi-ɗuminsa: Buhari ya sanya hannu a kan dokar harkokin man fetur

Daga AMINA YUSUF ALI

A yau Litinin, 16 ga watan Agusta, Shugaban Ƙasar Najeriya, Muhammadu Buhari, ya sanya wa ƙudurin harkokin man fetur hannu domin mai da shi doka.

Bayanin haka ya fito ne daga mai bai wa Buhari shawara na musamman a kan hulɗa da jama’a da kuma watsa labarai, Femi Adesina a Abuja.

Adesina ya ce hakan ya faru jim kaɗan bayan Shugaban ya dawo daga Landan a yayin da yake zaman killace kai na kwana biyar kamar yadda kwamitin tafiyar da harkokin yaƙi da annobar korona na Fadar Shugaban Ƙasa ya buƙata.

Ya ce Buhari ya rattaba hannu a kan dokar ne domin shauƙinsa na ganin ya sauke nauyin al’umma wanda Kundin Tsarin Mulkin Ƙasa ya rataya a masa.

A cewar Adeshina, sai Allah Ya kai mu Laraba mai zuwa ne bayan wa’adin killace kan Buharin ya cika za a cikata sauran tsare-tsaren da suke tattare da sabuwar dokar.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar 15 ga Yulin da ya gabata Majalisar Dattawa ta tura ƙudurin gaba, yayin da ita ma Majalisa Wakilai ta yi nata ɓangaren a ranar 16 ga Yulin 202, inda a wannan Litinin Buhari ya rattaba wa ƙudurin hannu.