Na yi tsufa da takarar sanata a 2023 – Masari

Daga AMINA YUSUF ALI

Gwamna Aminu Bello Masari na Jahar Katsina ya ƙaryata zargin cewa yana hararar wata kujerar mulkin bayan kammala wa’adin zangon mulkinsa na biyu a shekarar 2023.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wajen wani taro inda ya bayyana cewa, ya riga ya yi wa mutane hidima da dama a ɓangarori daban-daban a tsawon rayuwarsa. Don haka yanzu ba zai sake neman wani muƙamin ba sai dai ya tallafi matasa ‘yan baya su samu muƙamai a gwamnati. Amma sam shi ba zai ƙara neman muƙami ba, walau na gwamnati ko kuma na jam’iyya.

Ya ƙara da cewa, ” Na taɓa aiki tare da Majalisar Wakilai, inda na riƙe muƙamin kakakin majalisar, to me zan koma can na yi kuma?

“A jam’iyya kuma, na riƙe muƙamin mataimakin shugaban Jam’iyyar APC na Arewa, to wanne muƙami kuma zan koma na sake nema a Jam’iyyar kuma?”

A inda ya ƙara da cewa, a matakin jiha kuma ya kai matakin gwamnan jiha daga nan kuma bai san ina zai ƙara wucewa ba.

Don haka ya ce kamata ya yi a bai wa matasa dama su ma su dama su gwada sa’arsu su ma a fagen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *