Buni ya jagoranci gwamnonin APC don zawarcin Rashidi Ladoja a Ibadan

Daga AMINA YUSUF ALI

A Lahadin da ta gabata gwamnonin APC guda uku suka ziyarci Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, domin zawarcin dattijon jam’iiyyar PDP kuma tsohon gwamna, Alhaji Rashidi Ladoja, zuwa jam’iyya mai mulkin ƙasa ta APC.

Gwamnonin sun yi wannan tafiya ne a ƙarƙashin jagorancin Shugaban Kwamitin Riƙo na jam’iyyar APC, Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe. Har ila yau, Gwamnonin sun ziyarci wani babban mutum na Majalisar Dattijan Yarbawa, (YCE), Dakta Kunle Olajide. Sai kuma sarkin Musulmi na Ƙasar Yarabawa, Alhaji Dawud Akintola.

A tare da Mai Mala Buni akwai Gwamnan Jihar Kebbi, Atiku Bagudu da Gwamnan Jihar Jigawa, Abubakar Badaru, sai tsohon kakakin Majalisar Wakilai, Dimeji Bankole wanda bai jima ba da yin ƙaura i zuwa jam’iyyar APC.

Dukkansu sun haɗu a gidan Ladoja da ke titin Ondo da ke Unguwar Bodija, Ibadan a ƙarkashin jagorancin Sanata Fatai Buhari na Oyo ta Arewa, da kuma dattijon jam’iyyar APC Sharafadeen Alli. Sun samu awa guda suna ganawa kafin su wuce zuwa Akure, babban birnin Jihar Ondo.

Wata majiya ta bayyana cewa, gwamnonin sun tattauna yiwuwar dawowar Ladoja zuwa jam’iyyar APC da kuma yadda za a samar da kyakkyawan shugabanci a ƙasar nan don samun cigaba da kuma haɗin kai tsakanin ‘yan kasa. Inda suka yi nuni da shi Ladojan a matsayin wanda ya yi kuma aka gani aka yaba.

Zai iya ba da gudunmawa don samar da cigaba ko da bai fito takara ba. Kazalika gwamnonin sun nuna muhimmancin jihar Oyo a matsayin jigo mai ƙarfi a siyasar kudancin ƙasar nan. Shi ya sa suke neman sa da ya shigo APC.

A kan amsar ko zai amsa tayinsu ya shiga APC ko a’a, Ladoja dai bai ba da wata tsayayyar amsa ba, amma ya ce ya ji bayaninsu kuma zai duba ya gani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *