Hisbah ta kama matar aure da mutane biyar cikin otel a Kebbi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jami’an hukumar Hisbah a jihar Kebbi sun kama wasu mutane shida, ciki har da wata matar aure, bayan wani samame da suka kai wani otel da ke Birnin Kebbi kan zargin aikata ba daidai ba.

An gudanar da samamen ne a ranar 14 ga watan Mayu a wani otel da ke bayan masaukin Shugaban kasa a Birnin Kebbi, inda aka cafke maza uku da mata uku.

Daraktan Shari’a na hukumar Hisbah, Surajo Kamba ne ya tabbatar da kama mutanen cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a ranar Juma’a.

Ya ce, hukumar ta dauki matakin ne bayan samun bayanan sirri daga jama’a game da abubuwan da ake zargin suna faruwa a wurin.

Kamba ya ce bincike ya nuna cewa daya daga cikin matan da aka kama matar aure ce, yana mai cewa hakan na nuna bukatar kara tarbiyya da tsoron Allah a cikin al’umma.

Ya kara da cewa bincike na ci gaba kuma za a dauki matakin da ya dace da dokokin hukumar da na shari’a.

By Babaji