Kotu ta yanke mata hukuncin ɗaurin shekara 20 kan safarar makamai ga ‘yan ta’adda

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Babbar Kotun Tarayya a Abuja, ta yanke wa wata mata hukuncin ɗaurin shekaru 20 a gidan yari bisa samun ta da laifin safarar harsasan AK-47 302 ga ’yan bindiga.

Wata kotu a Abuja ta yanke wa wata mata hukuncin ɗaurin shekaru 20 a gidan yari bayan an kama ta da laifin safarar harsasan bindiga nau’in AK-47 guda 302 zuwa ga ’yan bindiga.

Rahotanni sun bayyana cewa an kama wacce ake tuhuma ne yayin da take ƙoƙarin kai wa masu aikata laifi harsasan domin tallafa musu wajen ayyukan ta’addanci.

Kotun ta ce hukuncin zai zama darasi ga duk masu shiga harkar safarar makamai ba bisa ƙa’ida ba, tana mai jaddada cewa gwamnati za ta ci gaba da yaƙi da masu taimaka wa ’yan ta’adda da duk wani nau’in laifi mai alaƙa da makamai.

By Babaji