Matatar Ɗangote ta maka gwamnatin Tinubu a kotu kan sabbin lasisin shigo da fetur

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kamfanin Matatar Man Fetur ta Ɗangote, ta maka Gwamnatin Tarayya a kotu akan cigaba da ba wa wasu ‘yan kasuwa da Babban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPC) lasisin shigo da man fetur daga ƙasashen waje.

A kwanan nan ne Hukumar Gudanarwar Man Fetur ta Ƙasa (NMDPRA) ta bada lasisi guda shida ga ‘yan kasuwa domin shigo da fetur Nijeriya don samar da wadataccen mai a ƙasa..

A cikin takardar ƙarar da matatar ta shigar, ta nemi kotun da ta haramta izinin shigo da fetur da aka ba NNPC da wasu ‘yan kasuwa da dama.

“Ɗangote ya bayyana cewa matatar mansa na da cikakken ƙarfin samar da isasshen man fetur da zai wadatar da Nijeriya baki ɗaya, yana mai cewa cigaba da shigo da mai daga waje na iya rage darajar matatar cikin gida tare da kawo cikas ga manufofin dogaro da kai a ɓangaren makamashi”, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

A shekarar 2025 ne Ɗangote ya janye shigar da irin ƙarar akan NNPC da wasu bayan Gwamnatin Tarayya ta tsoma baki.

By Babaji