Sojojin Amurka da Nijeriya sun halaka kwamandan ISIS a Sakkwato

Spread the love

Shugaba Donald Trump na Amurka ya sanar da halaka Abu-Bilal al-Minuki, wanda ake zargin na biyu a jagorancin kungiyar ISIS ta duniya, a wani samame da sojojin Najeriya da na Amurka suka gudanar a Najeriya.

Jaridar TheCable ta rawaito cewa, Trump ya bayyana cewa an kashe al-Minuki ne a wani farmaki mai sarkakiya da aka tsara cikin sirri, inda ya ce mutumin ya daina barazana ga Afirka da kuma taimakawa shirya hare-hare kan Amurkawa.

Ya kuma yaba wa gwamnatin Nijeriya bisa hadin gwiwar da ta bayar wajen gudanar da aikin.

Rahotanni sun ce hadin gwiwar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka ya karu bayan Amurka ta sake sanya Nijeriya cikin jerin kasashen da take sa ido a kansu kan batun tsaro.

A watan Maris, Amurka ta tura jiragen yaki marasa matuki da dakaru 200 zuwa Najeriya domin horaswa da bayar da bayanan sirri wajen yaki da ‘yan ta’adda.

Wannan na zuwa ne bayan hare-haren sama da Amurka ta kai kan maboyar ‘yan ISIS a jihar Sokoto a karshen shekarar da ta gabata.

By Babaji