HOTUNA: An yi jana’izar Janar Dzarma da wasu dakaru 7

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya jinjina wa sadaukarwar da dakarun suka nuna a halin rayuwarsu. Yayin da Gwamnan Adamawa, Umaru Ahmadu Fintiri ya sanya wa wata hanya a Yola sunan Marigayi Zurkushu don ci gaba da raya sunan.

Sanarwar da Daraktan sashen hulɗa da jama’a na sojojin Nijeriya, Brigadier General Onyema Nwachukwu ya fitar, ta nuna Buhari ya halarci jana’izar da aka gudanar a Yola a Juma’ar da ta gabata a bisa wakilcin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha.

Kazalika, sanarwar ta nuna Gwamna Fintiri ya bai wa iyalan Marigayi Brig Gen Dzarma Zurkushu tallafin kuɗi Naira miliyan 10, da kuma miliyan N17 ga iyalan sauran dakarun.

Boss Mustapha
Gwamna Fintiri