Yadda nacina ya kai ni ga nasara a gasar Hikayata, inji Zulaihat Alhassan

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Zulaihat Alhassan ita ce wadda ta zo ta uku a gasar Hikayata ta BBC Hausa ta shekarar 2021, wadda aka yi bikin karrama gwarazan jiya a Abuja, babban birnin tarayya.

Zulaihat ta kasance ta uku ne da labarin ta mai suna ‘Ramat’ wanda babban jigon sa yake ishara da gaskiya da riƙon amana, sai kuma ƙaramin jigon sa da ke bayar da labari akan fyaɗe.

Gwarzuwar ta uku ta kuma samu kyautar dala 500 tare da kambun karramawa.

Zulaihat Alhassan haifaffiyar garin Kaduna a yankin Maƙera da ke Kakuri cikin ƙaramar hukumar Kaduna ta Kudu. Ta yi makarantar firamare a Sabongarin Nasarawa II, sannan ta yi Sakandare a GGSS Kawo, daga bisani ta wuce Kwalejin Koyon Aikin Kiwon Lafiya da ke Tsafe, jihar Zamfara, inda ta karanci ɓangaren kula da lafiyar haƙora. Ta kuma ɗan tava aiki da wasu asibitoci kafin daga baya ta koma ta ci gaba da HND ɗin ta; duk a lokaci guda kuma tana taɓa kasuwanci, inji ta.

Zulaihat ta bayyana cewa tun tana ‘yar ƙarama take sha’awar karance-karancen littafan Hausa, wanda hakan ya ja ra’ayinta ga rubutu, inda ta ce mahaifiyarta ta sha ƙonawa da yaga littafan da take rubutawa ko karantawa.

Ta kuma bayyana cewa tana da naci akan rubutu da kuma sha’awar sa matuƙar gaske tun tana ‘yar ƙanƙanuwa kamar yadda ta bayyana.

Ta ƙara da cewa “akwai wata tsarata wadda da take ba ni tausayi saboda wasu abubuwa na rayuwa a tattare da ita, to akan ta na fara sha’awar gwada rubutu. Sai in sayo takarda da kuɗin da ake ba ni idan zan je Islamiyya in zo in raba dare in ta rubuta labarinta da abin da kuma wasu abubuwa da mutane ke yi da ya danganci irin rayuwar wannan baiwar Allah. To a nan rubutuna ya samo asali,” inji Zulaihat.

Haka zalika, Zulaihat ta ce ba ta taɓa rubutu a yanar gizo ba, ta bayyana cewa ta fi gane wa rubutu a takarda, hakan ya sa idan ta rubuta littafi sai ƙawayen ta da sauran ‘yan uwa su dinga amsa suna karantawa suna dawo mata da shi, kuma ba ta taɓa buga littafi ba.

Zulaihat ta kuma bayyana irin farin cikin da mahaifiyarta ta yi lokacin da ta sanar da ita cewa tana daga cikin mutane ukun da BBC ta fitar da sunayen su a gasar, kamar yadda ta kira ta a waya take shaida mata.

“Da na kira mahaifiyata a waya na ce ‘Hajiya littafan nan dai da kike ƙonawa da duka na akan su to yau dai sun yi nasara, na yi rubutu na tura BBC kuma ina ciki ukun da suka samu nasara, sai ta ke Ummi ina za ki kaini? Sai na yi dariya na ce ba inda zan kai ki Hajiya, rubutu na ne zai kai ki ni da ke. To irin kamar ma ba ta yarda da hakan ba, sai ta ce ‘Ummi kenan kina da nacin tsiya.”

Zulaihat Alhassan

Zulaihat Alhassan ta kuma yi kira ga marubuta musamman matasa irinta da su cire shakku da tsoro, su samu ƙarfin guiwa su sa a ransu duk abinda aka ce a zo a gwada, to ka gwada, don sai an gwada akan san na ƙwarai, kuma ko da ka gwada ba ka samu ba kar ka yi ƙasa a guiwa duk inda ka ji wata ka sake gwadawa.

Ta kuma shawarci marubuta manya da ƙanana da su dinga rubutu mai ma’ana da ilimantarwa ba wanda zai gurɓata tarbiyyar al’umma, al’ada ko cin mutuncin addin mu ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *