A ranar Laraba aka gudanar da jana’izar Sarkin Dutse, Marigayi Alhaji Nuhu Muhammad-Sanusi, wadda dubban jama’a daga sassa daban-daban suka halarta.
Marigayin ya rasu ne a ranar Talata a Abuja, sakamakon rashin lafiya, inda ya bar duniya yana da shekara 79.