Sabon salon yaƙin zaɓe: Tsakanin gidan Arewa da gidan Chatham

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Wani zanen hoton barkwanci da ɗan jaridar nan Bulama ya yi a jaridar Daily Trust cikin makon da ya gabata, ya nuna yadda wasu manyan ‘yan takarar shugaban ƙasa suka je Ingila, tsohuwar uwargijiyar Nijeriya, suka durƙusa a gaban Gidan Chatham suna roƙon a nuna goyon baya ga takarar da suke yi. Wannan hoto ne da ke isar da saƙonni masu muhimmanci ga ‘yan Nijeriya a yadda na kalle shi, kamar yadda shi wannan mai zanen barkwanci yake so ya nuna.

To, amma da farko kafin in yi sharhi game da wannan zane, yana da kyau mu fahimci menene ake nufi da Gidan Chatham, kuma wanne tasiri yake da shi ga siyasar duniya. To, shi dai wannan gida da ake kira da Chatham House, a turance, wata cibiya ce da gwamnatin ƙasar Ingila ta kafa domin nazari da tattauna al’amuran da suka shafi siyasar duniya, inda ake gayyatar manyan shugabanni, masana harkokin siyasa da masu faɗa a ji a harkokin siyasar ƙasashen duniya. Don gabatar da jawabai da shawarwari kan yadda za a warware wasu matsaloli da suka dabaibaye siyasar wasu ƙasashen, da neman goyon baya ga ƙasashen da suke da tasiri wajen juya al’amura a siyasance ko kuma ta harkar diflomasiyya.

Irin taruka da jawaban da ake gabatarwa su ne suke zama zakaran gwajin dafi ko kuma samar da wata alƙibla da za ta ja hankalin duniya da jama’ar qasashen da abin ya shafa, wajen nuna goyon baya ko akasin haka. Shi ya sa hankalin magabata a wannan babbar cibiya ta duniya ke kan Nijeriya da ke zaman ɗaya daga cikin manyan qasashe masu faɗa a ji a nahiyar Afirka da kuma a tsakanin ƙasashen da ƙarfin tattalin arziƙinsu ke tasowa, saboda ganin yadda ake samun cigaba da wayewa a siyasar ƙasar.

A wani ɓangare na shirye-shiryen tunkarar Babban Zaven 2023 da ke ƙara kusantowa, manyan ‘yan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyun APC, PDP, NNPP da kuma LP, wato Bola Ahmed Tinubu, Atiku Abubakar, Rabi’u Musa Kwankwaso, da Peter Obi, duk sun ziyarci wannan gida na Chatham House da ke Ingila, domin gabatar da manufofinsu da tsare-tsaren da suke da burin aiwatarwa idan suka samu damar samun shugabancin ‘yan Nijeriya sama da mutane miliyan ɗari biyu.

A lokacin da ɗan takarar muƙamin shugaban ƙasa ƙarƙashin Jam’iyyar APC Bola Tinubu ya ziyarci Chatham House a ranar 5 ga watan Disamba na shekarar 2022, ya gabatar da jawabi ne game da ƙudirorin da gwamnatin sa za ta fi mayar da hankali a kai idan ya samu nasara a Babban Zaɓen 2023, waɗanda suka haɗa da inganta tsaro, bunƙasa tattalin arziqi, da kyautata alaƙar Nijeriya da sauran ƙasashen duniya.

Sai dai kuma tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP wanda a baya lokacin Babban Zaven 2019 ya taɓa ziyartar gidan, bai amsa gayyatar da aka ce cibiyar ta yi masa ba, har kawo lokacin haɗa wannan rubutun, kamar yadda Daraktan Kula da Harkokin Afirka na Gidan Chatham, Alex Vines, ya tabbatar. Amma ko a waccan lokacin Atiku Abubakar ya mayar da hankali ne wajen bayyana shirin da yake da shi na farfaɗo da tattalin arzikin Nijeriya da bashi ya yi wa katutu, yayin da harkokin kasuwanci ke daɗa samun tasgaro a ƙasar.

Peter Obi, tsohon Gwamnan Jihar Anambra kuma ɗan takarar Jam’iyyar LP ya ziyarci gidan shi ma a makon da ya gabata, da gangamin neman goyon baya daga ‘yan Nijeriya da ‘yan siyasar duniya, don ya cimma ƙudirorin da yake ganin su ne za su kai ƙasar ga gaci, da suka haɗa da shawo kan ƙalubalen tsaro, samar da wadatar abinci a ƙasa, da bunƙasa harkokin kasuwanci da tattalin arziki.

Ɗan takarar Jam’iyyar NNPP Rabi’u Musa Kwankwaso, a jawabin da ya gabatar ya soki tsofaffin shugabannin Nijeriya tun daga shekarar 1999 da kasawa wajen shawo kan matsalolin rashin ayyukan yi ga miliyoyin matasan Nijeriya, magance ƙalubalen taɓarɓarewar tsaro, da yaqi da talauci da ke jefa rayuwar ‘yan Nijeriya cikin mawuyacin hali da hauhawar farashin kayan masarufi a rayuwa, inda yake cewa, zai yi amfani da gogewarsa a siyasa da mulki don ya ga ya dawo da kimar Nijeriya da walwala a rayuwar talakawan ƙasar nan, idan ya samu zama shugaban ƙasa a 2023.

Kodayake dokar zaɓen Nijeriya ba ta bada damar ‘yan Nijeriya da ke zaune a ƙasashen waje su kaɗa ƙuri’a ba, kuma akasarin mahalarta taron da ake yi a wannan gida ba waɗanda ke da katin yin zaɓe a Nijeriya ba ne, ballantana jawaban da ake yi a taron ya canza ra’ayin wasu su zaɓi wani daga cikin ‘yan takarar da suke rububin zuwa Ingila don gabatar da jawabi a Chatham House, masana na ganin zuwan nasu na da tasiri ne kawai ta fuskar diflomasiyya da kuma bai wa manyan manazarta harkokin siyasar duniya damar yadda za su fahimci ingancinsa da ƙwarewar sa wajen sanin makamar yadda zai shugabanci ƙasar da ake yi wa kallon giwar Afirka. Sannan har wa yau sharhin da manazartan za su yi daga baya game da ƙudirorin da ya gabatar musu, na iya yin tasiri a wajen ‘yan bokon Nijeriya da ke da ruwa da tsaki kan harkokin zaɓe da siyasar ƙasar.

Ganawa da ƙwararru da masana ko ƙungiyoyin al’umma a keɓance wani salo ne da ‘yan siyasa suke amfani da shi a duniya, saɓanin irin wanda aka saba na shiga kasuwanni da ƙauyuka ana hawa durom ana faɗar maganganu na jan hankali da alƙawuran bogi, wanda wasu ma shaci faɗi ne kawai, don dai talakawa su samu abin yawo da shi a baki suna yaɗawa da kwaɗaitar da masu zaɓe. Sai dai yanzu abubuwa sun canja, an samu wayewa da canji a tsarin yaqin neman zaɓe. Duk da kasancewar har yanzu ana shiga ƙauyuka da birane don gangamin taron jama’a da neman goyon baya, ƙari a kan haka shi ne na yadda ‘yan takara kan nemi damar ganawa da wasu masu faɗa a ji, ƙungiyoyin al’umma, sarakuna da magabata, har da ƙungiyoyin mata da matasa, inda suke zama da su a keɓance suna bayyana musu manufofin su da tanadin da suke da shi na yadda za su shawo kan matsalolin da ke damun talakawa, da kuma amsa wasu muhimman tambayoyi daga mahalarta taron, ko kuma karɓar shawarwari.

Akwai kuma taruka da ake yi a manyan cibiyoyin taro na yankuna da ake tattauna cigaban dimukraɗiyya da siyasar yankin, don bai wa masu ruwa da tsaki na yankin damar ganawa da ‘yan takara gaba da gaba, da kuma bayyana masa buƙatunsu a matsayin al’umma, da sharaɗin da za su gindaya wa kowanne ɗan takara, don ganin ya yi musu ayyuka ko shigar da ƙwararrunsu da ‘yan siyasar su cikin tafiyar da gwamnati, idan an samu nasara.

Har wa yau akwai kuma taron muhawara na ‘yan takara da ake da wasu ƙungiyoyi masu qarfin faɗa a ji a harkar watsa labarai, ko Gamayyar Ƙungiyoyin Jama’a da Ma’aikata, don auna ƙwarewa da cancantar ‘yan takara a fannoni daban-daban na shugabanci da harkokin siyasar duniya, da sanin yadda za a shawo kan wasu matsaloli da ke addabar al’umma.

Misalin Gidan Chatham a Ingila shi ne Gidan Arewa a Kaduna, wanda ya yake zaman wata cibiya ta tattauna matsaloli da muhimman batutuwan da, suka shafi Arewa, al’ummar ta. A yayin da harkokin siyasa da batun zaɓuka suka tunkaro, Gidan Arewa shi ma na karɓar na sa rabon, inda ake ganin zarya da kai komon ‘yan siyasa da ke zuwa don tattauna wa da masana da ƙwararru, da manyan ƙungiyoyin masu faɗa a ji, da suka haɗa da ƙungiyar Tuntuɓa ta ACF, da Gidauniyar Tunawa da Sardaunan Sakkwato Firimiyan Arewa, Majalisar Dattijan Arewa, Jam’iyyar Matan Arewa da Cibiyar Bincike da Haɓɓaka Tarihin Arewa ke shiryawa, waɗanda ke haɗuwa su gayyaci manyan ‘yan takara daga jam’iyyu daban-daban, don bayyana manufofin su da tanade tanadensu ga al’ummar Arewa. Hakan wata dama ce gare su ta tallata kansu da neman goyon baya daga muhimman ƙungiyoyin al’umma na yankin.

A wannan kakar siyasar ma haka aka yi, yayin da Babban Ɗakin Taron Gidan Arewa mai ɗaukar mutane kimanin dubu 3 ya tarbi wasu manyan ‘yan takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin shirin ƙawancen haɗin gwiwa na ƙungiyoyin Arewa, da suka haɗa da Kola Abiola na Jam’iyyar PRP, da Prince Adewale Adeboye na Jam’iyyar SDP, da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar daga Jam’iyyar PDP, sai kuma Bola Tinubu na Jam’iyyar APC da Peter Obi na LP.

Kola Abiola na PRP ya bayyana cewa idan an ba shi haɗin kai da goyon baya a zaɓen 2023 zai yi ƙoƙarin kawo haɗin kai a tsakanin ‘yan Nijeriya, bunƙasa harkokin kasuwanci, inganta tsaro da samar da ayyukan yi don yaqi da talauci da cin hanci da rashawa. Ya kuma bayyana buƙatar a riƙa bai wa masu jini a jika musamman matasa damar shiga harkokin siyasa da shugabanci don su kawo sabbin dabaru da tsare-tsare na zamani da za su taimaka a sauya fasalin ƙasar nan.

Shi kuwa, tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, ya ɗora nasa gangamin goyon bayan ne, kan wasu ƙudirori biyar da yake so ya sa a gaba, da suka haɗa da samar da haɗin kan ƙasa, bunƙasa tattalin arziki, ƙarfafa darajar ilimi, farfaɗo da ayyukan Ƙananan Hukumomi da ƙara ƙarfin iko a hannun jihohi. Yayin da ya ce, idan an zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa, zai tabbatar kowanne ɗan Nijeriya ya samu ‘yancin rayuwa da walwala a ko’ina a faɗin Ƙasar nan ba tare da tsangwama ko nuna wariya ba.

Ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da tanadin sa da alqawuran abubuwan da yake so ya yi wa Arewa, da suka haɗa da warware matsalar tsaro, da almajiranci, tare da ƙaddamar da kundin tsarin ayyukan da ya ce ya tanadarwa Nijeriya.

Haka shi ma ɗan takarar Jam’iyyar LP Peter Obi, lokacin da ya ziyarci Gidan Arewa a Kaduna ya shaida wa Arewa cewa, zai kawo sauye-sauyen da za su kawo wa al’ummar wannan yankin musamman a ɓangaren yaƙi da talauci, ayyukan gona da tsaro. Ya kuma bayyana ƙwarin gwiwarsa na ganin idan aka samar da ayyukan yi za a rage zaman banza a tsakanin matasa, wanda yake ganin yana daga dalilan da suke angiza matsalolin tsaro a yankin.

Rahotanni sun bayyana cewa, ɗan takarar Jam’iyyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso, bai samu zuwa wannan tattaunawa ta Gidan Arewa ba, saboda zargin da ya yi cewa, akwai yunƙurin marawa wani ɗan takara ɗaya baya, maimakon a bai wa kowa damar bayyana manufofin sa da bai wa ‘yan Nijeriya damar bin zaɓin da suke so. Wannan na daga cikin ƙalubalen da irin waɗannan ƙungiyoyin ke fuskanta kenan na kasa voye manufofinsu na siyasa, don haka dole zarge-zarge irin wannan su yi ta fito, da kuma zargin karvar wasu kuɗaɗen, don nuna goyon bayan su ga wani ɗan takara a ƙungiyance.

Lallai yana da kyau ‘yan siyasa su cigaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki, da ƙungiyoyin da suka cancanta kuma suke da tasiri ba ‘yan handama da kasuwancin yaqin neman zaɓe ba, daga wannan jam’iyya suna waccan, in ba su samu a wajen wannan ba, gobe ka gansu a gindin wancan ɗan takara suna zaginsa. Ba masu kafa ƙungiyoyi don lokacin siyasa ba, ba kuma ƙungiyoyi na raba kan jama’a ba. Ko malamai ‘yan ci da addini, da masu rawanin da ba sa riƙe girman su.

Idan ‘yan siyasa na neman goyon baya to, ‘yan Nijeriya za su bibiya ba turawa ba, tare da aiki da masana da manazarta na cikin gida ba waɗanda suke bakin ganga ba. Ko waɗanda za su yabe ka a kan idonka, sai ka ba su kuɗi sun dafe a koma wajen abokin adawarka ana hulɗa da shi don samun wata mamora daga wajensa. Sannan a riƙa kiyaye abin da za a faɗa a wajen yaƙin neman zaɓe, ban da shirya ƙarya da yaudara da alƙawarin bogi, ko faɗar abin da mutum ya san ba zai iya ba, ko ba shi da ƙwarewa a kai. Hakan yana zubar wa da ɗan siyasa kima da mutunci. A kaucewa kalamai na tunzura jama’a, da kawo rabuwar kai, ko ɓangaranci a wajen yaƙin neman zaɓe.

Ba zuwa Chatham House ko Arewa House ne kaɗai abin dubawa ba, me ka tanada don kawo gyara a ƙasa, idan ka samu nasara, ko idan jama’a sun amince da kai sun baka amana, ta yaya za ka sarrafa arzikin qasa ta yadda jama’a za su ji daɗin mulkin ka. Kowanne ɓangare ya san yana da rawar takawa a cikin gwamnati, kuma yana ganin amfanin gwamnati a rayuwarsa.