Hukuma ta gargaɗi masu fassara fina-finan ƙetare

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Tace Fina-finai ta Ƙasa reshen Arewa maso Yamma, ta gargaɗi masu dobin, fassarawa da safarar fina-finan ƙetare ta haramtacciyar hanya da su gaggauta barin wannan harka.

Gargaɗin na ƙunshe ne cikin sanarwar da hukumar ta fitar mai ɗauke da kwanan wata 15 ga Nuwamba da kuma sa hannun Jami’i mai kula da harkokin hukumar a shiyyar Arewa maso Yamma, Umar G. Fage.

Hukumar ta ce fassara fina-finan ƙetare zuwa harsunan gida ba bisa ƙa’ida ba laifi ne da ya saɓa wa sassa na 25(1), 33(1), 56 da 5(1) na Kundin Dokokin hukumar na 1993.

Wannan hali in ji hukumar, na haifar da ɓarna ga Masana’antar Fina-finai ta Nijeriya da Hukumar Tace Fina-finai ta Ƙasa.

A cewar hukumar, tana da hurumin ba da lasisi ga waɗanda suka dace, tace fina-finai, sanya ido kan tabbatar da ana kiyaye dokoki a masana’antar fina-finai yadda ya dace da sauransu.

Ta ce doka ce babu wanda zai gudanar da harkar dobin ko fassarar fina-finai, ko baje kolin fina-finai da makamantansu face sai ya samu lasisi daga hukumar.