Jami’an hukumar ‘yan sandan farin kaya sun kashe ɗaya tare da kama wani daga cikin waɗanda suka yi garkuwa da Hajiya Hauwa’u Adamu, mahaifiyar fitaccen mawaƙin siyasan nan, Dauda Rarara.
In bamu manta ba, wasu ‘yan bindiga sun shiga gidan mahaifiyar Rarara da ke ƙauyen Kahutu a ƙaramar hukumar Ɗanja a Jihar Katsina, inda suka yi garkuwa da ita a ranar Juma’a 28 ga watan Yuni, 2024.
Sai dai ta samu ‘yanci bayan ta shafe kwanaki 20 a tsare.
Wata majiya mai ƙarfi a hukumar ta shaida wa Jaridar Aminiya cewa an kuma gano Naira miliyan 26.5 a wani samame da aka yi a boye.
Majiyar ta ce, rundunar hukumar farin kaya, bisa sahihan bayanan sirri, ta kama wasu gungun ‘yan bindiga biyar a dajin Maƙarfi inda suke raba kudin fansa.
“Hamisu Tukur,yanzu haka yana hannun jami’an tsaro da raunin harbin bindiga, yayin da Bature ya mutu,” in ji majiyar.
