
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Tawagar shugabannin Majalisar Wakilai ta ziyarci matatar Ɗangote da ke Lekki a jihar Legas, ƙarƙashin jagorancin kakakin majalisar, Tajudeen Abbas.
Attajirin da ya fi kowa kuɗi a Afirka kuma shugaban kamfanin Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote da wasu manyan ma’aikatan matatar su ka tarbi tawagar inda ƴan majalisar yayin dubiyar matatar da ka iya fidda ganga 650,000 a kullum.
Wannan shi ne karo na biyu da su ke ziyartar matatar cikin wata biyu ganin cewa tana shirin fara aikin samar man fetur a wata mai zuwa da kuma ƙalubale da take samu daga kamfanonin kasashen waje kan samun ɗanyen mai domin sarrafawa.
A watan Yuni ne shugaban majalisar dattijai, Godswill Akpabio da tawagarsa su ka kai irin ziyarar ga matatar inda ya yaba wa aikin da kuma nuna goyon bayansu ganin cewa matatun jihohi sun gaza fara aiki tare da sharhi ga muhimmancin samuwarta a cikin al’umma.
