Zanga-zanga: Ana so a yi amfani da matasa wajen ɓata sunan yankinmu  – Hon El-Abuja

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Ƙungiyar ‘APC Northwest Ambassadors’, Hon Shamsudden Shu’aibu El-Abuja ya gargaɗi al’ummar Arewacin Nijeriya musamman matasa akan zangar-zangar tsadar rayuwa da ake shirin yi ƙarshen wannan watan.

Hon. Shu’abu El-Abuja ya ce ana son yin amfani da al’ummar yankin Arewa ne kawai wajen ɓata sunan yankin, inda ya nuna cewa dole matasa suka zuciya nesa tare da ƙara juriya da haƙuri.

“Idan matasan Nijeriya musamma ‘yan Arewa  suka yi nazari, kawai ana son yin amfani da mu ne wajen ɓata sunan yankinmu.

“Nasan cewa kun yi haƙuri iya haƙuri, kun raka amma har yanzu matsalar yau da ban ta gobe daban, hakan ya sa kuka harzuƙa.

“Kowa ya san ni ɗan gwagwarmaya ne, amma ba na so a jefa matasan Nijeriya cikin wani hali, saboda da yawan sun san abinda suke yi,” inji shi.

Hon El-Abuja ya ƙara da cewa tsbbas al’ummar Nijeriya suna buƙatar ɗauki daga gwamnatin Tarayya da ta jihohi, sanatoci da ‘yan majalisun tarayya musamman wajen tashi tsaye don inganta rayuwar al’umma da rage musu raɗaɗin tsadar rayuwar da ake fama da ita.

‘Ina kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da gwamnoninmu da ‘yan majalisunmu akan su ji tsoron Allah su dubi halin da talakawa ke ciki a ƙasar nan. Ka da ku manta talakawan su suka zaɓeku har kuka kai wannan matsayi, amma kowane matsahi ya zama ɗan kallo,” ya ce.

By ukarofi