Hukumar Kwastom ta kama fasinja da ta dawo daga Saudiyya da sama da dala miliyan ɗaya a filin jirgin Aminu Kano

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Kwastom ta Nijeriya (NCS) ta kama $1,154,900 da SR135,900 da ba a tantance ba a filin jirgin saman Mallam Aminu Kano (MAKIA) da ke jihar Kano.

Kakakin Hukumar NCS, Abdullahi Maiwada, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis.

Ya ce an kama su ne a kwanan baya a lokacin duba kaya da aka saba yi inda suka samu wata fasinja mai suna Hauwa Ibrahim Abdullahi da ta dawo daga Saudiyya a jirgi mai lamba SV401.

A cewar Maiwada, a yayin gwajin jikin fasinja da jami’an NCS suka gudanar, an gano kuɗin da ba a bayyana ba a ɓoye a cikin fakitin dabino.

Ya bayyana cewa, wannan ya yi daidai da ƙudurin NCS na aiwatar da ƙa’idojin hada-hadar kuɗi da kuma hana safarar kuɗaɗen haram a kan iyakokin Nijeriya.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “A bisa tsarin da aka kafa, an miƙa wadda ake zargin da kuma kuɗaɗen ƙasashen waje da aka kama zuwa ga hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) domin ci gaba da bincike da kuma ɗaukar matakin shari’a.”

“Daga baya, kotu ta yanke wa wadda ake tuhuma hukunci kamar yadda ake tuhumarta da kuma bayar da umarnin a ƙwace kuɗaɗen da ba a bayyanawa Gwamnatin Tarayya ba kamar yadda dokar ta 2022 ta tanadar da ƙudin haram.

“A ƙarƙashin jagorancin Kwanturola-Janar na Hukumar Kwastom, Bashir Adewale Adeniyi, Hukumar NCS ta ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da aikinta na yaƙi da fasa-ƙwauri, hada-hadar kuɗi da sauran laifukan kan iyaka.

“Wannan sabon kame yana nuna sadaukarwar da ma’aikatar ta yi don kare muradun tattalin arzikin ƙasa da kuma tabbatar da bin ƙa’idojin kuɗi.

“Hukumar NCS za ta ci gaba da haɗa kai da hukumomin gwamnati da masu ruwa da tsaki don ƙarfafa tsaron kan iyaka, da inganta bin dokokin kuɗi, da kuma kare tattalin arzikin Nijeriya.

“An shawarci matafiya da masu ruwa da tsaki a fannin hada-hadar kuɗi da su kasance cikin taka-tsan-tsan kuma a koyaushe su dinga bin ƙa’idojin kuɗi na halal,” inji shi.

By ukarofi