Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Majalisar Wakilan Nijeriya ta amince da sabon ƙudirin dokar sake fasalin haraji a ƙasar guda huɗu da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatar a baya-bayan nan, yayin da ta yi nazari tare da amincewa da rahoton kwamitinta na musamman kan shawarwarin a ranar Alhamis 13 ga Maris, 2025.
ƙudirorin sun haɗa da Dokar Samar da Kima, Tattarawa da kuma ƙididdigar Kuɗi don Tara Kuɗi ga Tarayya, Jihohi da ƙananan Hukumomi; Bayar da Iko da Ayyukan hukumomin haraji, da kuma abubuwan da ke da alaƙa da su, da kuma daftarin dokar da za ta soke Dokar Tattalin Arzikin ƙasa ta ƙasa, Doka ta 13, 2007 da ƙaddamar da Dokar Ma’aikatar Harajin Nijeriya don Kafa Ma’aikatar Harajin Nijeriya.
Sauran sun haɗa da ƙudirin dokar kafa hukumar tattara kuɗazen shiga ta haɗin gwiwa, kotun ɗaukaka ƙara ta haraji da kuma ofishin kula da haraji, don daidaitawa harkokin haraji.
Da yake miƙa rahoton domin a duba shi, shugaban kwamitin kuzi, James Faleke, ya ce an yi taka-tsan-tsan domin a magance matsalolin da suka shafi jama’a.
