Rashin bin ƙa’ida: WHO ta cire Nijeriya a ƙasashen da za ta bai wa tallafin rigakafin maleriya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Nijeriya ba ta cikin jerin ƙasashen da su ke kan hanyar samun allurar rigakafin cutar zazzaɓin cizon sauro daga Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) saboda ƙarancin iya aiki da ababen more rayuwa da ta ke bai wa ƙasar, lamarin da ke ƙara nuna damuwa game da kiwon lafiyar ƙasar na dogon lokaci.

Cibiyar Kula da Cututtuka ta Afirka (ACDC) kwanan nan ta bayyana cewa ƙasashen Afirka guda uku daga Masar, Ghana da Tanzaniya sun shirya don tabbatar da cancantar WHO na samun rigakafin maleriya guda takwas don wadata kasuwannin nahiyar tsakanin 2025 da 2030. Wannan wani babban ci gaba ne kan yunƙurin nahiyar na samun wadatuwa wajen samar da allurar rigakafi, inji ACDC.

Cibiyar ta yi nuni da cewa, shekaru biyar masu zuwa za su taka muhimmiyar rawa wajen haɓaka samar da rigakafin.

Godwin Ntadom, kodinetan shirin kawar da cutar zazzaɓin cizon sauro na ƙasa, ya shaida wa menama labarai hakan bayan wani taron masu ruwa da tsaki kan samar da allurar rigakafin zazzaɓin cizon sauro a Abuja ranar Talata cewa Nijeriya ba ta cikin ƙasashen guda uku da cibiyar Africa CDC ta amince da su.

Ntadom, wanda ya wakilci Muhammad Pate, mai kula da harkokin lafiya da walwalar jama’a a wurin taron, ya ce: “Kamfanonin uku ba daga Nijeriya su ke ba. Sun ambaci Masar, Ghana, ina jin na uku Tanzania ko makamancin haka, amma Nijeriya ma tana kan hanyar samun na ta,” inji shi.

By ukarofi