Tinubu ya sauya sunan Jami’ar Ilimi ta Tarayya a Kano zuwa Yusuf Maitama Sule

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya canja sunan Jami’ar Ilimi ta Tarayya da ke Kano zuwa Jami’ar Ilimi ta Tarayya ta Yusuf Maitama Sule.

Alhaji Sule, 1929 – 2017, ya bayar da gudunmawa sosai ga ci gaban zamantakewa da siyasar Nijeriya a duk tsawon rayuwarsa.

Ya yi aiki a matsayin wakilin Nijeriya na dindindin a Majalisar ɗinkin Duniya a New York, inda ya kasance Shugaban Kwamitin Musamman na Majalisar ɗinkin Duniya kan Yaƙi da Wariyar Launin Fata.

Ya kuma yi aiki a matsayin Mai Tsawatarwa na Majalisar Wakilai ta Tarayya tsakanin 1954 zuwa 1959, jagoran tawagar Nijeriya a taron ƙasashe ’Yan Ba Ruwanmu a 1960, Kwamishinan ƙorafe-ƙorafen Jama’a na Tarayya na Farko (1976) da kuma Ministan Ma’adinai da Makamashi.

Shugaba Tinubu ya ce, ya yi imanin cewa, gadon Ambasada Sule zai zaburar da matasa masu tasowa wajen tabbatar da gaskiya, kishin ƙasa da halayyan ƙwarai.

Jami’ar Ilimi ta Tarayya da ke Kano na ɗaya daga cikin manyan jami’o’in ilimi guda bakwai a ƙarƙashin Gwamnatin Tarayya a faɗin ƙasar. Tun farko Gwamnatin Jihar Kano ce ta mallake ta.

A matsayinta na jami’ar ilimi ta tarayya, za ta ci gaba da taka rawar gani wajen horar da malamai da ƙarfafa fannin ilimi a Nijeriya.

By ukarofi