Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa, ya gana da tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari kafin ya bar jam’iyyar All Progressiɓes Congress (APC).
Blueprint Manhaja ta tuna cewa, El-Rufai ya sanar da sauya sheƙa zuwa jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook da aka tabbatar a ranar Litinin.
Yayin da ya ke magana a wata hira da sashen Hausa na BBC a ranar Laraba, ya bayyana cewa, ya tuntuɓi Buhari kafin ya ɗauki matakin, inda ya jaddada cewa ya kan nemi shawarar tsohon shugaban kan harkokin siyasa.
A cewarsa, “Akwai wasu mutanen da kafinna yi wani babban abu ko yanke shawara, na tuntuɓa, kuma duk abin da suka ce kada na yi, ba na yi, kuma tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yana cikinsu.
“Na tuntuɓi Buhari kafin na bar APC. A ranar Juma’a ne na je na same shi. Da ƙyar na yanke wata babbar shawara ba tare da tuntuɓar shi ba. Sai na ce masa ya yi mini addu’a, ya kuma yi sa min albarka.”
El-Rufai ya tuno da al’amuran da ya faru a lokacin da yake gwamna a lokacin da ya nemi amincewar Buhari kan wasu muhimman muƙamai da suka haɗa da miƙa sunayen kwamishinoninsa domin tantancewa.
“Ko a lokacin da na ke gwamnan Kaduna, kafin na naɗa kwamishinonina, na kai wa Buhari jerin sunayen ne, domin ya duba ko daga cikinsu akwai wanda ya taɓa zagin sa.
“Ya yi dariya, ya yi min godiya, sannan ya ce, min za ka iya ci gaba da naɗa kwamishinoni.”
