Hukumar Raya Kogunan Hadeja da Jama’are ta yi bikin Ranar Koguna ta Duniya

Spread the love

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano

Ranar Lahadin ƙarshen watan Satumba ce ranar da Majalisar ɗinkin Duniya ta ware, domin bikin Ranar Kogunan Duniya, domin wayar da kan jama’a kan muhimmancin koguna da ƙoramai ga cigaban al’umma. A wannan rana hukumomin ruwa, masana’antu da ƙungiyoyi masu kula da muhalli kan gudanar da bukukuwa, domin ƙara ilimantar da jama’a kan kula da lafiyar koguna.

A bana, Hukumar Kula da Raya Kogunan Haɗeja da Jama’are ta shirya taron faɗakarwa a Fadar Koma da ke ƙaramar Hukumar Wudil a Jihar Kano, inda aka gabatar da lakcoci da tattaunawa kan alfanun koguna. Shugaban hukumar, Injiniya Rabiu Suleiman Bichi, ya bayyana cewa, Nijeriya ta fara shiga cikin ƙasashen da ke bikin wannan rana shekaru huɗu da suka gabata, inda a Jihar Kano aka fara bikin a Fadar ’Yan Danko kusa da kogin Chalawa.

Injiniya Bichi ya ce manufar bikin ita ce wayar da kai kan muhimmancin ruwa da koguna, musamman ganin yadda ambaliyar ruwa ke kawo illa a sassan ƙasar. Ya yi kira da a kare koguna ta hanyar guje wa zubar da shara da bayan gida a cikinsu, domin hakan kan jawo cututtuka da asarar rayuka da dukiyoyi.

Ya kuma danganta buƙatar kula da koguna da shirin Renewed Hope Agenda na Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu, wanda ke mai da hankali kan bunkasa noman rani da samar da wadataccen abinci. A cewarsa, hukumar na daukar matakai domin gyara wuraren noman rani da suka lalace, tare da mayar da su matsayin tushen samar da abinci.

A nasa jawabin, ƙwararre kan ilimin ruwa, Injiniya Yahaya Dalha Kazaure, ya jaddada cewa ruwa daga koguna baya tsaya ga sha da noma kadai ba, har ma ana amfani da shi wajen samar da wutar lantarki, wanda ke taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa tattalin arzikin ƙasa. Ya yi gargadi ga mazauna yankunan koguna da su guji zubar da tarkace ko gurbatattun sinadarai a cikin ruwa.

Bayan kammala taron, Injiniya Bichi ya kai ziyara gonakin rani na hukumar a kan hanyar Wudil, musamman wajen da ake kira Sangai ko Sprinkler Farm, inda aka gano matsalar hana ruwa isa gonaki saboda rashin isasshiyar wutar lantarki. Ya tabbatar da cewa hukumar ta fara aiki da masana da kamfanonin wuta don kawo gyara, domin tabbatar da ɗorewar noma da wadatar abinci a ƙasar.

By ukarofi