Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnatin Jihar Neja ta gargaɗi mazauna wasu yankuna da ke bakin Kogin Neja da Kogin Kaduna da su koma wuraren da suka fi aminci bayan an fara sakin ruwa daga manyan dam-dam na ruwa a jihar.
Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA) ce ta fitar da wannan gargadi a cikin wata sanarwa da Darakta-Janar ɗinta, Abdullahi Baba-Arah, ya sanya wa hannu a ranar Alhamis.
Baba-Arah ya bayyana cewa lamarin ya biyo bayan sakin ruwa da ake yi daga dam-dam na Kainji, Shiroro, Zungeru, da Jebba.
A cewarsa, “Ma’aikatar Kula da Ruwa ta ƙasa ta gargadi al’ummomin da ke bakin kogunan Neja da Kaduna da su koma wuraren da suka fi aminci. Dam-dam ɗin na sakin dubban galan na ruwa a minti, wanda zai iya haifar da tumbatsar kogunan.
“Saboda haka, gwamnatin jiha na shawartar al’ummominmu da su takaita duk wani aiki a bakin koguna a wannan lokacin ruwan sama domin kauce wa ambaliya. Mutanen da ke zaune a yankunan bakin ruwa su koma wuraren da aka riga aka ayyana masu aminci,” inji sanarwar.
