Hukumar Zakka da Waƙafi a Jihar Kano ta yanke nisabin zakka, diyyar rai da sadakin aure

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano

Hukumar Zakka ta Hubusi ta Jihar Kano haɗin gwiwa da hukumar Shara’a da majalisar Malamai da ta Limaman Juma’a da kuma ƙungiyar ma’aikatan Zakka da Wakafi ta ƙasa sun amince da Naira dubu ashirin (20,000.00) a matsayin mafi ƙarancin nisabin sadakin aure.

Haka kuma sun amince da Naira miliyan ɗari da hamsin (150,000,000.00) a matsayin diyyar wanda ya kashe rai bisa kuskure da kuma naira dubu ɗari tara da tamanin da biyar (985,000.00) a matsayin nisabin zakka.

Farfesa Aliyu Tahiru Muhammad, Malami a Jami’ar Bayero dake Kano kuma babban Sakataren ƙungiyar masu aikin Zakka da wakafi ta ƙasa ne ya bayyana hakan a jawabin bayan taro da hukumar Shara’a ta Jihar Kano da Takwararta ta Zakka da kungiyar Limaman masallatan juma’a da majalisar Malamai ta Jihar Kano da kungiyar ma’aikatan Zakka da wakafi ta kasa da sauran masu ruwa da tsaki suka gabatar, taron wanda ya gudana a Kano a Alhamis din nan.

“Abubuwan da aka amince da su a wannan taro sune kamar haka:

Taron ya amince da amfani da Durham a matsayin ma’aunin nisabin Zakka a jihar Kano wanda kimarsa ta kai naira dubu ɗari tara da tamanin da biyar a yau.

Zaman ya amince cewa Sadaki yarjejeniya ce tsakanin waliyan yarinya da wakilan Ango wanda za suyi la’akari da wadatar mai Aure da Kimar wacce za’a aura da halin da ake ciki, amma duk yarjejeniyar da za suyi kada sadakin ya Gaza naira dubu asirin.

Diyyar rai ta kama naira miliyan dari da hamsin. Amma ga wanda ya yi kisan ganganci, za’a koma ga mataki mafi tsauri, wanda Alkali zai fitar da shi a wajen yin hukunci.

Za a riƙa yin wannan zama duk bayan wata uku domin yin duba ga wannan batutuwa.

Za a sanar da gwamnatin wacce zata kirawo taron wayar da kai da na ‘yan Jaridu da kuma isarwa ta hanyar da duk ta dace. Hakazalika suma sauran majalisar Malamai da hukumomin da abin ya shafa zasu taimaka wajen isar da sakon.

Tun da farko, shugaban hukumar Zakka da Hubusi ta Jihar Kano Barista Habibu Muhammad ɗan-Almajiri ya ce daukar matakin ya biyo bayan yadda a lokutan daban-daban Malamai ke bada mabanbantan Bafawoyi game da nisabin zakka da sadaki da biyan Diyyar Rai.

ɗan-Almajiri ya yi fatan Malamai a fadin Jihar Kano za su taimaka wajen Dabbaka matsayar da aka cimma.

By ukarofi