Hukumomin samar da haraji na bin Gwamnatin Tarayya Tiriliyan N3, inji FAAC

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Asusun Kasafin Kuɗin Nijeriya, FAAC, ya bayyyana cewa, Gwamnatin Tarayya za ta iya fuskantar asarar Naira Tiriliyan 2.97 da Dala Miliyan 36.33 idan hukumomin samar da kuɗaɗen shiga a ƙasar nan ba su daidaita kuɗaɗen shiga da aka tara ba.

Adadin da wasu hukumomin da ba a bayyana sunayensu ke bin Gwamnatin Tarayya tun daga watan Afrilun 2024 an bayyana shi ne a lokacin taron kwamitin Asusun Kasafin Kuɗin Nijeriya.

Mataimakin shugaban kwamitin da ya wakilci shugaban kwamitin Kabir Mashi a wajen taron ya ce, ana cigaba da ƙoƙarin sasantawa da hukumomin da abin ya shafa a wajen taron sulhu na wata-wata.

Ya bayyana cewaɗ an samu kudin shiga na Niara Tiriliyan 1.143, inda aka samo biliyan N157.183 daga kuɗin doka, sai biliyan N463.425 da aka samu na harajin VAT.

Ya ƙara da cewa, an samu kuɗin shiga nan Naira Biliyan 15.146 daga harajin kuɗin saƙon aika kuɗi ta wayar hannu (EMTL) da biliyan N507.456 na harajin da aka samu daga musayar kuɗin ƙasashen waje.

Asusun FAAC ya tabbatar da samun kuɗin shiga da ya kai Naira Tiriliyan 2.32 a watan Mayu.

Ya bayyana cewa, “Bayanin kuɗaɗen na tarayya da ya taso daga taron sasantawa tsakanin hukumomin da aka gudanar a cikin Afrilu 2024: Mataimakin Shugaban, PMSC ya bada rahoton cewa jimlar adadin da ba a warware ba saboda asusun daga taron sulhun da aka yi tare da Hukumomin Samar da Kuɗaɗen shiga daga Afrilu 2024 ya kai Dala 36,329,376.24 da Naira 2,977,561,881,021.29.”

Ya bayyana cewa, duk wasu maƙudan kuɗace daga RGA kafin watan Yunin 2023 an miƙa su ga kwamitin sulhu na masu ruwa da tsaki kuma PMSC yana jiran sakamakon sulhun.

Da ya ke tsokaci, shugaban kwamitin kwamishinan kuɗi na jihar Ekiti, Akintunde Oyebode, ya yaba wa hukumar ta PMSC bisa ƙoƙarin da take yi na kwato wasu maƙudan kuɗaɗe mallakin asusun kasafin kuɗin tarayya tare da sanar da cewa Ƙananan hukumomin na jin irin tasirin da aka samu wajen farfaɗo da tattalin arzikin kasa.