Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa Mai Zaman Kanta (ICPC) ta fara gudanar da WANI bincike kan Babbar Sakatariyar Ma’aikata a Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai ta Tarayyar Nijeriya, Binyerem Ukaire, kan zargin dakatar da fitar da kuɗaɗen da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince a bai wa wasu manyan hukumomin gwamnati.
A wani rahoto da jaridar Preminum Times ta fitar, ta ce, wannan mataki na ICPC ya zo ne kwanaki biyu kacal bayan wata rahoto ya bayyana cewa Ukaire ta riƙe takardun biyan kuɗaɗen da aka ware domin gudanar da ayyukan hukumomin da ke ƙarƙashin kulawar ma’aikatar.
Rahoton ya ce, kuɗaɗen da Shugaba Tinubu ya amince da su an tanade su ne domin tallafa wa ayyukan Hukumar Talabijin ta Nijeriya (NTA), Kamfanin Rediyon Tarayya na Nijeriya (FRCN), Muryar Nijeriya (VON), Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN), Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta ƙasa (NOA) da kuma Hukumar Kula da Gidajen Rediyo da Talabijin ta ƙasa (NBC).
Majiyoyin da suka san yadda lamarin ya gudana sun bayyana cewa Ukaire ta ƙi ci gaba da aiwatar da biyan kuɗaɗen ne saboda shugabannin hukumomin sun ƙi amincewa da buƙatarta ta gabatar mata da cikakken bayani kan ayyukan da suke gudanarwa da kuma yadda suke kashe kuɗaɗensu.
Sai dai shugabannin hukumomin da wasu ƙwararru a aikin gwamnati sun bayyana cewa irin wannan buƙata ta saɓa wa ƙa’idojin aikin gwamnati.
Sun yi nuni da wata takarda da Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF) ya fitar, wadda ta umarci ma’aikatun da ke kula da hukumomi da kada su tsoma baki cikin harkokin kuɗaɗen hukumomin, domin hukumomin na da alhakin kai rahoto ga kwamitocin gudanarwarsu da kuma ministocinsu.
Bayan ƙorafe-ƙorafen da suka biyo baya, ICPC ta gayyaci tare da yi wa Binyerem Ukaire da shugabannin hukumomin tambayoyi domin gano dalilin da ya sa aka dakatar da fitar da kuɗaɗen.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa, duk da ci gaba da binciken, ba a tsare Babbar Sakatariyar Ma’aikatar ko kuma shugabannin hukumomin bayan kammala yi musu tambayoyi ba.
Rahotanni sun nuna cewa bayan hankalin jama’a ya koma kan batun, Ukaire ta amince da takardun biyan kuɗaɗen tare da tura su domin a fara aiwatar da biyan.
A lokacin da aka tuntuɓi shugabannin hukumomin a ranar Asabar, sun tabbatar da cewa an tura takardun kuma yanzu ana jiran a saki kuɗaɗen zuwa asusun hukumominsu.
