Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wani jami’in leƙen asirin Rundunar Sojin Nijeriya mai muƙamin kanar, Abdussalam A. Ude, ya rasa ransa bayan ya yi gumurzu da wasu ‘yan bindiga da suka kai masa hari domin yin garkuwa da shi a gidansa da ke unguwar Kurudu a Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Majiyoyi sun ce, marigayin, wanda ɗan asalin Jihar Enugu ne, na daga cikin ƙwararrun jami’an leƙen asirin soji, kuma ana sa ran za a ƙara masa girma zuwa muƙamin Birgediya Janar a shekara mai zuwa.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kai masa farmaki ne da yammacin ranar Litinin, jim kaɗan bayan ya isa gidansa. Ana zargin sun buɗe masa wuta ne lokacin da yake fitowa daga cikin motarsa.
Bayan harin, ‘yan bindigar sun yi yunƙurin yin garkuwa da Kanar Ude, amma ya ƙi miƙa wuya. Duk da cewa maharan sun fi shi yawa, ya yi ƙoƙarin kare kansa da iyalansa tare da tunkarar maharan.
Majiyoyin tsaro sun ce juriyar da ya nuna ta hana maharan tafiya da shi da rai, lamarin da ya sa suka riƙa harbinsa ta kusa har ya mutu.
A yayin harin, maharan sun kuma harbe wasu daga cikin mutanen gidansa, ciki har da matarsa, direbansa da jami’in tsaron gidansa. Dukkansu sun samu raunukan harbin bindiga kuma an garzaya da su asibiti domin ci gaba da jinya.
Wata majiya mai kusanci da binciken ta bayyana Kanar Ude a matsayin jajirtaccen jami’in leƙen asiri wanda ya nuna jarumtaka da kwarin gwiwa har zuwa lokacin da ya rasa ransa.
Majiyar ta ce, “Sun so su yi garkuwa da shi, amma ya yi tsayuwa tsayin daka ya ƙi bin su. Abin takaici, hakan ya jawo aka kashe shi.”
A halin yanzu, hukumomin tsaro sun fara gudanar da bincike domin gano waɗanda suka aikata wannan hari tare da kamo su domin su fuskanci hukunci.
Kafin rasuwarsa, Kanar Ude ya riƙe muhimman mukamai a fannin leƙen asirin soji da yaƙi da ta’addanci a Rundunar Sojin Nijeriya.
Ya kuma taka rawa a hare-haren da aka gudanar kan ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya, baya ga wasu ayyukan haɗin gwiwar tsaro da ya gudanar a ƙasashen Chadi da Faransa.
An shirya gudanar da jana’izarsa a Masallacin Mambilla da ke Abuja ranar Talata, bisa koyarwar addinin Musulunci.
Kisan jami’in ya sake tayar da hankalin jama’a kan yadda hare-hare ke ci gaba da addabar jami’an soji masu aiki da waɗanda suka yi ritaya, musamman a Babban Birnin Tarayya.
Lamarin ya tunatar da kisan Birgediya Janar Uwem Harold Udokwere mai ritaya, wanda aka kashe a ranar 22 ga Yunin 2024 bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari gidansa da ke Sunshine Homes Estate a yankin Lokogoma na Abuja.
A wancan harin, marigayin ya yi ƙoƙarin kare iyalansa kafin maharan suka kashe shi tare da tserewa da bindigarsa da wasu kayayyaki masu daraja.
Masana harkokin tsaro sun ce sabon harin na iya ƙara matsa lamba kan gwamnati da hukumomin tsaro su ƙara tsaurara matakan kariya ga jami’an soji masu aiki da waɗanda suka yi ritaya, musamman waɗanda suka taɓa riƙe muhimman mukamai a fannin tsaro da leƙen asiri.
