Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya tabbatar da cewa sake fasalin hukumomin tsaro da yadda ake gudanar da ayyukansu zai haifar da gagarumar nasara a yaƙin da ake yi da ta’addanci, ‘yan fashi daji da masu garkuwa da mutane a faɗin Nijeriya.
Tinubu ya bayyana hakan ne ranar Talata a Fadar Shugaban ƙasa da ke Abuja yayin da ya karɓi baƙuncin shugabannin Taron Manyan Limaman Cocin Katolika na Nijeriya (CBCN) ƙarƙashin jagorancin shugabansa, Archbishop Matthew Ndagoso na Kaduna. Taron ya samu halartar manyan limaman cocin guda 19.
Shugaban ƙasar ya ce, gwamnatinsa na sake tsara tsarin tsaron ƙasa domin ƙara inganta yadda hukumomin tsaro ke gudanar da ayyukansu ta hanyar bunƙasa tattara bayanan sirri, sake fasalin cibiyoyin tsaro, samar da ingantattun kayan aiki da kuma inganta walwalar jami’an da ke bakin daga.
Ya buƙaci shugabannin addinai da su riƙa amfani da mimbari wajen yin Allah wadai da hare-haren ta’addanci tare da ƙarfafa mabiyansu su mara wa gwamnati baya wajen kawo ƙarshen rashin tsaro.
“Ba mu da wata ƙasa face Nijeriya. Dole ne mu haɗa kai domin ci gabanta. Na amince da faɗaɗa rundunonin soji, muna sayen sabbin kayan yaƙi tare da gina sababbin barikoki. Za mu kawar da ta’addanci,” inji shugaban ƙasar.
Da yake magana kan rage talauci, Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen da ke inganta rayuwar jama’a, ciki har da Asusun Lamunin Ilimi na Nijeriya (NELFUND).
Ya ce, lokacin da ya karɓi mulki, ƙasar na fuskantar matsanancin ƙalubalen tattalin arziki da fargabar durƙushewar tattalin arziki, amma yanzu an samu daidaito.
“A yau zan iya tabbatar muku cewa tattalin arzikin Nijeriya ya dawo kan hanya. Mun ceto ƙasar daga barazanar durƙushewa, kuma alamun ci gaba sun fara bayyana. Rayuwar jama’a na ci gaba da ingantuwa,” inji shi.
Tinubu ya ƙara da cewa ya gaji nasarori da matsalolin gwamnatin da ta gabace shi, amma gwamnatinsa ta yi aiki tukuru wajen daidaita tattalin arziki da samar da kyakkyawan fata ga ‘yan ƙasa.
Ya kuma buƙaci matasa da sauran ‘yan Nijeriya su rungumi ilimi, koyon sana’o’i da kasuwanci domin cin gajiyar damar da gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu ke samarwa.
A cewarsa, haɗin kan ƙasa, zaman lafiya da ci gaban Nijeriya wajibi ne da kowa ya ba su muhimmanci.
Shugaban ƙasar ya yi nuni da cewa zaman lafiya ya fara bayyana a fannin ilimi, yana mai cewa ɗalibai na kammala karatunsu a kan lokaci saboda rashin yajin aikin ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU).
“Yanzu karatun digiri na shekara huɗu yana ɗaukar shekara huɗu. ASUU ba ta yajin aiki. Wannan ma amsar addu’a ce,” inji shi.
Da yake magana kan zaɓen 2027, Tinubu ya ce Hukumar Zaɓe ta ƙasa Mai Zaman Kanta (INEC) na gudanar da aikinta cikin adalci ba tare da nuna son kai ba.
Ya ce dukkan jam’iyyun siyasa suna da damar shiga zaɓe ba tare da tsangwama ba, yana mai cewa masu ƙorafi wataƙila tsoron rashin ƙarfi ne ke damunsu.
Har ila yau, shugaban ƙasar ya ce gwamnonin jihohi ne ke da ikon yanke hukunci kan mayar da makarantun mishan ga masu su bisa tanadin kundin tsarin mulki.
Ya tuna cewa lokacin da yake gwamnan Legas ya mayar da dukkan makarantun mishan ga masu su.
Tinubu ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa ta amince da kafa ƙarin jami’o’i domin biyan buƙatar karatun gaba da sakandare, yana mai cewa bayanan Hukumar Kula da Jami’o’i ta ƙasa (NUC) za su taimaka wajen tsara kasafin kuɗin NELFUND.
A nasa jawabin, Shugaban CBCN, Archbishop Matthew Ndagoso, ya gode wa shugaban ƙasar bisa kyakkyawar tarbar da ya yi wa wakilin Fafaroma mai kula da hulɗar ƙasashe, Archbishop Paul Gallagher, yayin bikin cika shekara 50 da ƙulla alaƙar diflomasiyya tsakanin Nijeriya da Fadar Batican.
Sai dai ya bayyana damuwarsa kan matsalolin tsaro, talauci, ƙarancin guraben karatu a manyan makarantu da kuma buƙatar tabbatar da sahihanci da adalci a zaɓen shekarar 2027.
Ya kuma roƙi gwamnatin tarayya ta duba batun mayar da makarantun mishan tare da tabbatar da adalci ga duk masu ibada wajen samar musu da wuraren gudanar da ibadarsu ba tare da nuna bambanci ba.
Archbishop Ndagoso ya ce ɗaya daga cikin manyan abubuwan da za su zama tarihi a mulkin Tinubu shi ne ƙarfafa cibiyoyin dimokuraɗiyya da tabbatar da sahihin zaɓe a ƙasar.
